*Zaki iya samun zuciyar namiji da kyawawan halayyan ki, saboda namiji tamkar jariri ne idan har kika iya tafiyar dashi,irin hakan za'a dinga ganin tamkar kin mallake sa ne,wasu har suyi zaton ko ta wani hanya kika mallake sa,nan ko ba wata hanya ba ce illa kyawawan halayyan ki,kina kuma son duk abinda yake so,sannan kina masa biyayya.*
*In har mace zata yiwa Namiji biyayya, zatana kiyaye abinda baya so zasu zauna lafiya a tsakanin su,kafin aji kan su za'a jima koda ace sabani zasu samu,amma ba zai wani dauki lokaci ba, saboda sun riga sun san kan su,kuma sun fahimci junan su.*
*Mace yar kwalisa da iya ado shima na tasiri a zuciyar Namiji,wannan ado yana matukar daukar hankali Namiji,wannan ma sirri ne babba,don haka yan uwa mata ku gane ku rike sirrin iya ado da kwalisa.*
©️Abeeda usman


0 Comments