Maganin gyaran Nono na mata,wanda yake kara girma,da kuma yadda ake ragewa

 








Maganin gyaran Nono na mata,wanda yake kara girma,da kuma yadda ake ragewa



Maganin gyaran Nono na mata,wanda yake kara girma,da kuma yadda ake rage:

SHARE 🌾
Domin gyara nono ga mata

Idan baku mantaba munyi muku alkawarin zamu kawo muku bayani akan yadda zaku magance zubewar nono masamman awajen mata waenda suke kasada shekaru 39 yrs.

Saboda mahimmancin gyaran jiki awajen mata masamman ma gyaran nono munkawo muku bayanai akan yanayin gyaran nono, aciki mun ambaci cewa gyaran nono yakasu kashi uku:

🌾- Nafarko shine karin girman nono.


Nabiyu shine rage girman nono

🌾- Na’uku shine mikar da nono.

Munyi bayani akan nafarko yau kuma zamuyi bayani akan na ukun wanda shine yadda za’a magance matsalar zubewar nono awaje mata masu karancin she karu, har yanzu sai abimu bashin nabiyun zuwa wani lokaci akusa.

Hakikanin gaskiya kowace mace tanaso taga tanada tsayayyen nono tsawon rayuwanta amma kash.. Saide hakan ba maiyuwa bane, sabida zubewar nono adabi’ance yana faruwa tareda tafiyan shekaru.

Maganin sanyin kowanne iri

kamar yadda aka sani duk lokacinda mace takai shekaru arba’in to gaskiya babu abinda zaihana nononta zubewa, saide matsalan ana iya samun dayawa mata wanda basukai wannan shekarunba kuma nononsu yazube, sannan yana daga cikin abubuwanda yake janyo zubewar nono kamar:

🤶- shayarwa.

🤶- Daukan ciki.

🤶- Yankewar jinin haila gabadaya.

🤶- Ramewa cikin dan kankanin lokaci.

🤶- Kiba.

🤶- Wasu cututtuka kamar cancer dasauransu.

Atakaice zamu fadi hanyoyi guda uku na mikarda nono batareda shan wahala ko kashe kudiba, nafarko:

1- Asamu kankara ashafa ajikin nonuwan duka biyu, ake shafawa ahankali har tashafa ako’ina har natsawon kamar minti biyu, za’a maimaita hakan na tsawon wasu kwanaki, kankara yanada tasiri sosai wajen matse nono da hanashi zubewa, amma kada yawuce minti uku tana shafawa daga bisani sai tasamu bra dedenta tasaka.

2- Nabiyu kuwa shine man zaitun, dayawa yan’uwa mata suna tareda man zaitun amma suna neman maganin zubewar nono, to wallahi kinbar magani mai mahimmanci sosai, anaso ki milke nononki daman zaitun kullum safe dayamma kishafa da hankali sannan atake kisaka bra wanda yadace dake. Za’a maimaita haka nawasu kwanaki, kuma za’a iya amfani da zaitu Lawz ko jojoba oil amadadin man zaitun.

3- Na’uku za’a iya hada neem oil tareda garin ruman cokali daya agarwaya wannan hadin sai adaura akan garwashi yadanyi zafi kadan sai asauke abarshi yahuce, daga bisani sai ake shafawa nonon sau biyu ayini zuwa wasu kwanaki kadan kuma wannan hadin yanada tasiri sosai.

 

Za’a iya amfanida kowanne daga cikin waennan hanya guda uku kuma kowanne yanada tasiri insha Allah

 

Rikicin Kasar Sudan Abin Damuwa Ne Musamman Ga Hausawa Musulmi Yan Arewacin Najeriya.

Ku kunsan: Akwai Hausawa miliyan Shida a kasar Sudan, inda galibinsu mabiya addinin Musulunci ne, kuma Wasunsu suna jin yarensu Hausa na asali maimakon Larabci. Yawancinsu suna rayuwa ne ta hanyar Sana’ar noma a yankin Darfur, Da jihar Al-Jazira da kuma jahohin Kassala da ke gabacin Gedaref da Sennar da Blue Nile.

Ƙididdigar mutane da aka yi a 1993 ta nuna akwai mutum miliyan 30 a Sudan, amma tun bayan wannan lokacin ba a sake yin wata ƙididdiga ba – musamman saboda yaƙin basasar ƙasar da aka dade ana yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta yawan ƴan ƙasar sun kai miliyan 37, inda ita kuma hukumar leƙen asiri ta Amurka, CIA ke cewa sun kai miliyan 45.

Amma bayan da Sudan Ta Kudu ta ɓalle daga ƙasar, ana ƙiyasta yawan ƴan Sudan ya kai miliyan 42.

Duk da cewa Sudan ta shafe gomman shekaru ƙarƙashin tsarin mulki na Shari’ar Musulunci, ƙasar na bin tsarin karatu iri biyu ne kamar yadda lamarin yake a Najeriya da Nijar.

Akwai makarantun boko da kuma na addinin Musulunci, ciki har da na allo.

A makarantun boko ana koyar da ɗalibai darussa ne da harshen Larabci, kuma su kan koyi darussa kamar Lissafi da kimiyya da fasaha da kuma harsuna kamar turancin Ingilishi da Faransanci.

Yadda Hausawa suka kasance a Sudan

Masana tarihi sun bayyana cewa Hausawa sun isa yankin da ake kira Sudan ne a yanzu tun farko zuwan addinin Musulunci yankin Afirka Ta Yamma.

Wasunsu sun tafi Sudan ne saboda dalilai na kasuwanci, wasu kuma saboda Aikin Hajji ne – inda wasunsu suka tafi a ƙafa, wasu kuma a bisa dawaki da jakuna.

Yawancin Hausawan da suka yi wannan tafiya sun tashi daga yankin arewacin Najeriya da kudancin Nijar ne, inda suka riƙa bi ta cikin yankin da a yau ke cikin ƙasashen Kamaru da Chadi Afirka Ta Tsakiya.

Sun riƙa sauka A zango a wasu wurare kan hanyarsu ta zuwa kasa mai tsarki. Wasu daga cikin wuraren da suka sauka sun zama garuruwan Hausawa sannu a hankali.

Wasu Hausawan ba su sami damar isa ƙasa mai tsarki ba, shi ya sa suka yi zamansu a duk yankunan da suka sami kansu.

Wadannan yankunan yanzu na cikin ƙasashe irin su Chadi da Eritrea da Habasha da ƙasar Afirka Ta Tsakiya.

Wannan ne ya sa har zuwa yau waɗannan zangwanni na nan cikin ƙasashen da Hausawa suka riƙa bi gabanin su isa gabar Tekun Bahar maliya, ko Bahar al-Ahmar da Larabci.

Hausawan da suka yi karatun boko kuma suka dade suna shiga ayyukan gwamnati kamar Dakta Waheeb Ibrahim Haroun wanda shi kwararren likitan mata ne da ke aiki a ciki da wajen Sudan saboda kwarewarsa. Yana da takardun digiri fiye da biyar a fannonin kiwon lafiya.

Akwai wata sanata mai suna Dakta Maryam Abdulkarim Muhammad Ahmad, wadda asalinta malamar makaranta ce, amma ta shiga harkokin siyasa tun daga matakin jiha.

An fara zabarta ga muƙamin ƴar majalisar jiha kafin daga baya aka zaɓe ta zuwa majalisar ƙasar a matsayin ƴar majalisar dattawa, wanda ita ce mace Bahaushiya ta farko da ta taɓa riƙe wannan muƙamin a Sudan.

Akwai kuma Muhammad Abdallah Bin Jaws wanda ya daɗe yana aikin diflomasiyya a ƙasar.

Amma mutumin da yafi yin fice cikin dukkan Hausawa Sudan shi ne Fadl Sishshi Ayib wanda ya so ya jagoranci ƙasar amma hakan bai yiwu ba saboda hambare gwamnatin Omar al Bashir da aka yi a 2019. Shi ya ajiye aikinsa domin raɗin kansa domin ya tsaya takara.

Akwai kuma Jalal Rabeh wanda wazirin tsohon shugaba Omar al Bashir ne a gwamnatin da ta shude.

Akwai Muhammad Abdallah, wanda shi babban jakadan Sudan a ƙasashe kamar Hadaddiyar Daular Larabawa, da Abdallah Muhammad Musa da Al Tayyib Rabeh wadanda ƴan majalisar dattawan Sudan ne su.

Akwai kuma Muhammad Sharaqaddeen wanda shi kuma alkalin kotun ƙolin Sudan ne.

A halin yanzu matasan Hausawa da yawansu na karatun boko kuma dubbansu na ayyukan gwamnati da suka haɗa da aiki soja da na ƴan sanda.

Sana’o’in Hausawan Sudan

Kamar yadda aka san Bahaushen ƙasar Hausa, a Sudan ma Hausawa sun riƙe sana’ao’in da aka san su suna yi kaka da kakanni.

Manyan sana’o’in Hausawa sun haɗa da noma da kiwo da kasuwanci da kuma karatu da karantar da addinin Musulunci kamar karantar da Al Ƙur’ani.

Akwai kuma wasunsu da ke ayyukan kwadago kamar gini da ɗaukar kaya da wanki da guga da tuƙin mota. Sai dai zuwan zamani ya sa sun rungumi sana’o’i irin na zamani kamar na aikin ofis da na gwamnati. Akwai kuma wasunsu da suka shiga siyasa kuma sun yi nisa sosai cikinta.

Akwai kuma Hausawa masu yawa da suka shiga aikin ƴan sanda da na soji, baya ga waɗanda ke aiki a kamfanonin sadarwa irinsu Sudani da Zain ada kuma Areeba.

Akwai kuma mata masu sana’ar dafe-dafen abinci irin na Hausawa kamar tuwo da miyar taushe da na Larabawa kamar tuwon gero da miyar tagaliyya (aseeda) da kisre da fuul da wani nau’in kosai mai suna ɗa’amiyya.

Akwai manya da ƙananan malaman makarantar boko a Sudan da suka shahara, baya ga likitoci da manyan ƴan kasuwa, kamar Abubakar Idris (Abu Zaituna).

Akwai kuma shaharraun malaman addinin Musulunci kamar Sheikh Abdullahi Hamza na Damazin, mutumin jihar Blue Nile, wanda malamin darikar Tijjaniyya ne.

Hausawan Sudan kuma na da kungiyoyi na wasan kwaikwayo a faɗin ƙasar inda suke bayyana al’adunsu da basirar da ubangiji yayi mu su. Cikin fitattun ƴan wasan kwaikwayo akwai Abu Nujoom da ƙungiyarsa.

A bangaren waƙe-waƙe da kaɗe-kaɗe kuwa, ba a bar Hausawa a baya ba. Akwai shahararrun mawaƙan Hausa kamar Abdurraheem Wad al Gadaref da har yanzu ke waƙa da harshen Hausa. Sai dai wasunsu kamar Babiker Hindi da Maryam ƴar Andalus na gwamawa – inda suke yin wasu waƙokin da Larabci, wasu kuma da Hausa.

Al’adun Hausawan Sudan

Hausawan Sudan sun rabu kashi biyu ne, domin akwai waɗanda suke zaune wuri guda bayan sun isa ƙasar, akwai kuma waɗanda suka gauraya kansu da Larabawa.

Hausawan da ke zaune zallarsu a garuruwansu sun ci gaba da al’adun ƴan uwansu na Najeriya da Nijar, amma waɗanda suka shige cikin Larabawa na bin al’adun Larabawa ne.

A misali, Hausawan da ke bin al’adun kakanninsu na yin bukukuwan suna da na aure tamkar yadda ake yi a Najeriya da Nijar. Bayan kwana bakwai a kan yi wa jariri suna da tsaga irin ta ƙasar da kakanninsa suka fito.

Matar da ta haihu a karon farko kan tafi gidan iyayenta ne, kuma a kan yi wa jariri aski ranar suna.

Su kuma Hausawan da suka shiga cikin Larabawa ba sa yin suna bayan kwana bakwai, ba sa yi wa jariri aski ranar suna kuma ba sa tura mace gidan iyayenta bayan ta haihu, ko da kuwa haihuwar farko ce.

A ɓangaren abinci, Hausawa na cikin dukkan abincin da ƴan uwansu na Yamma ke ci kamar tuwo da fura da nono da kunu da sauransu.

Wani abin sha’awa shi ne a Sudan, Hausawa sun shahara wajen sarrafa nama su mayar da shi balangu ko tsire. Sai dai a can ba a kiransa da tsire sai dai ‘a gashe’.

Sai dai wasu Hausawan da suka rungumi al’adun Larabawa kan ci abincinsu waɗanda suka haɗa da eyish (biredi) da aseeda da kisre da madara (laban).

Ta Bangaren tufafi kuwa, da wuya ka sami Bahaushen Sudan yana sanya riguna kamar babbar riga da wando ko kaftani ko kuma ƴar shara ga maza, mata kuma ba su cika daura zannuwa irin na matan Hausawa ba.

Yawancin mazansu sun fi sanya tufafin Larabawa wato farar jallabiyya mai fadin hannu da rawani, inda matansu kuma ke sanya tobe – wanda matan bare-bari kan ɗaura da aka fi sani da lafaya.

Bikin aure


Post a Comment

0 Comments