Dole Sai Ango Yayi Jima’i Da Wata Yar Uwar Amarya An Gwada Kwazonsa Kafin A Bashi Aure.
Wata al’adar da wasu mutane ke yi ya yin da aka ɗaura auren budurwa a yankinsu ta bukatar gwajin budurci daga amarya da kuma karfin iyawa daga ango wanda za a gwada shi da goggon amarya.
Al’ummar Banyakole a ƙasar Uganda suna da wata Al’ada wacce idan za a miki aure tilas ne gwogginki ta zama miki babbar ƙawa saboda ƙauna da soyayya da kuma jagorantar ƴar uwarta ta hanyar zama aminiya ga ƴar yayarta musamman kan abubuwan da ba za ta iya rabawa da mahaifiyarta ba.
Domin a wajen ƙabilar Banyakole na Uganda, aikin inna ya wuce yin nasiha kawai har ma da ɗaukar duk wani nauyi da ya gagari amarya ta yi shi tare da mahaifiyarta a al’adance.
Mutanen Banyakole wadanda kuma ake kira da kabilar Ankole mazauna Masarautar Bantu ce wacce ta samo asali tun daga karni na 15. Tana cikin Kudu maso Yammacin Uganda, gabas da Tafkin Edward, masarautar da Sarki Mugabe ke mulki wacce ta shahara da kare haƙƙin aure na musamman.
Auren Banyakole
Aure a cikin wannan al’ada yana da mahimmancin gaske yayin da iyaye ke samun farin ciki da alfahari daga auren ƴaƴansu. A bisa al’adar Banyakole, idan yarinya ta kai shekara takwas ko tara, aikin inna ne ta gyara ta don rayuwar iyali. Gwoggon ta za ta koya mata duk wani abu daya kamata ta sani game da matsayinta na mace mafi mahimmanci, a matsayin matar aure.
Budurci a cikin wannan al’ada ana girmama shi sosai don haka dole ne ƴan mata su kauracewa yin jima’i kafin aure. Kuma idan aka gano yarinya ba budurwa ba ce kafin aure, to za ta fuskanci hukuncin kisa ko yanke mata hukunci daga al’umma.
Bugu da ƙari, mutanen Ankole suna ɗaukar wasu hanyoyi na gyara budurcin yaransu, dan haka lokacin da ƴan mata suka kai shekaru takwas ko tara, ana bukatar su riƙa yin kitso inda ake ciyar da su gero, naman shanu, da madara. Ana yin wannan galibi don ƴan mata ko sa sami damar jawo hankalin miji.
Auren Banyakole ya ƙunshi shagulgula da dama ciki har da lokacin bayar da kyauta da aka sani da “Kuhingira” inda dangi da abokan amarya ke gabatar mata da kyaututtuka kamar shanu da sauran kayan abinci da za su kai gidanta na aure. Inda bayan kwanaki 10, ana aiwatar da wata al’ada wacce ake kira Okukoza Omunuriro. A nan ne za a sanya Amarya ta ɗora girki ta kunna wutar girkin ta na farko a sabon gidan Mijinta.
A ranar daurin aure, ana shirya biki a gidan amarya inda mahaifin zai yanka bijimi yayin da a gidan ango kuma akwai wani biki na kara aure. Amma da farko, dole ne a yi bikin gargajiya na karshe, bikin da ya kunshi gwaje-gwaje biyu wanda dole ne goggon amarya ta gudanar da shi.
Tunda budurci shine ma’aunin aure ga matan ƙabilar Banyakole, dole ne kowace amarya a gwada ta da innarta don tabbatar da budurcinta kafin auren. Idan amarya ta wuce gwajin budurci, ana zaton ba ta da ilimin jima’i ko yadda za ta faranta wa sabon mijinta rai ta hanyar jima’i.
Don haka, gwaji na biyu ya shafi goggon amarya tana gwada ƙarfin jima’in da ango ke da shi ta hanyar yin lalata da shi. A yayin wannan aikin da ake yi a gaban Amarya tana kuma koyon duk dabarun Jima’i da kuma sifofin da aka fi so don ta iya ba wa mijinta gamsuwar da ake buƙata a matsayin ta na Amarya don faranta wa mijinta rai a cikin auren.
0 Comments