Kalli sana’o’in wasu jaruman kannywood kafin su shigo harkar film, abin zai baku mamaki

 



Kalli sana’o’in wasu jaruman kannywood kafin su shigo harkar film, abin zai baku mamaki.


Zamu iya cewa kashi 90 cikin 100 ma jaruman kannywood akwai wata sana’ar da suke yi sannan suka samu damr shigar matsana’antar kannywood hakan yasa muka bincike muku wasu sana’o’i da wasu jaruman kannywood suka yi kamin su shigo matsana’antar film.


Ta kasance daya daga cikin jaruman da suka sha wahala sosai kamin su samu daukaka a yadda ake ganin su a yanzu, yanzu dai ta kasance daya daga cikin manyan jaruman kannywood mata da suka fi kudi, jarumar haifaffiyar kasar gabon a baya ta kasance Malamar makaranta ce a kasar gabon daga bisa ni tabar karantarwar tazo kasar Nijeriya ta shigo masana’antar film ta kannywood.


Ta kasance daya daga cikin jaruman da suka sha wahala sosai kamin su samu daukaka a yadda ake ganin su a yanzu, yanzu dai ta kasance daya daga cikin manyan jaruman kannywood mata da suka fi kudi, jarumar haifaffiyar kasar gabon a baya ta kasance Malamar makaranta ce a kasar gabon daga bisa ni tabar karantarwar tazo kasar Nijeriya ta shigo masana’antar film ta kannywood.


MARYAM YAHAYA


Matashiyar jarumar kannywood da ta shigo matsana’antar ta kannywood a lokacin da take tashen balaga kuma ta shigo matsana’antar ne da kafar dama inda ta samu daukaka cikin kankanin lokaci, ita dai a baya kamin a fara sakata Film a lokacin da tazo kallon yan film, ta kasance tana saida awara a bakin kofar gidan su wanda da yawa daga cikin mutanen suka santa kamin ta fara harkar film suka shaida.


ADO GWANJA


Mawakin mata da a duniyar hausawan yanzu babu wani mawakin mata da ya kaishi, kamar yadda wani malami ya faɗa tunda yacewa mata ” sama ” har yanzu fa basu sauko ba. Mawakin yayi suna ne a shekaru hudu da suka gabata bayan ya fito a film din dan kuka a matsayin wanda yake jan ragamar shirin, a wata hira da aka taba yi da shi ya tabbar da cewa shi sana’ar “shayi” yake kamin ya sunduma matsana’antar kannywood, kuma sana’ar shayin nan gabon gidan su ne, kamin mahaifinsa ya rasu har sarkin kano yana sawa a siyo masa shayi daga wajen su.


HAMISU BREAKER


Babban mawakin kannywood mamalankin wakar “Jaruma” da yayi sanadiyar haska shi a duniya, mawakin dai yanzu Allah ya sanya shi cikin manyan mawakin kannywood da suka yi kudi cikin kankanin lokaci a harkar waka, dama shi waka haka yake idan kayo Sa’a kayi wata waka da ta sanu karbuwa sosai a wajen jama’a tofa sai muce ka karka ta yanke saka, shi dai mawakin kamin a sanshi a harkar waka sosai, ya bayyacewa cewa shi tela ne wato dinkin kaya yake.

Post a Comment

0 Comments