Kalli gurin da mata suke matukar so a taba ajikin su yayin jima’i .....











Rashin ƙarfi mazakuta, wani babban kalubale ne da maza ke fuskanta a wannnan zmani, ba tare da la’akari da shekarunsu ba. Akwai al’amura da yawa dake haifar da matsalar daurin azzakari ga maza da su ka hada da, yanayin kiwon lafiya, matsalolin zamantakewa, shan wasu nau’ikan magunguna, shan sigari, shan magunguna barkatai, shan barasa da sauran su.

 

Baya ga abubuwan da muka zana a sama dake haifar da raunin mazakuta, matsala a kwakwalwa, kamar damuwa, bacin rai, na haddasa raunin azzakari.


Ana iya cewa mutum ya hadu da wanan matsala ta raunin mazakuta idan yana daya daga cikin abubuwan nan uku.

 

1. Rashin sha’awar jima’i

2. Rashin mikewar azzakari

3. Rashin dadewar azzakarin a tsaye.

 

Hakika wani bincike ya gano cewa, samari da yawa na ziyartar likita ne saboda matsalar rashin karfin azzakari. Sau da yawa, maza masu fama da matsalar ciwon sukari, cututtukan zuciya, hawan jini, ko yawan kiba, na iya kamuwa da rashin karfin maza ba tare da sun sani ba.

 

Idan ba a dauki mataki da wuri ba, raunin mazakuta kan haifar da wasu matsalolin, kamar rashin gamsuwa yayin jima’i da rashin gamsar da iyali, jin kaskanci, damuwa, da kuma matsalolin zamantakewar aure. Hakanan, mai wannan matsala na iya fuskantar barazanar rashin samun haihuwa.


Yanza mu jero hanyoyin maganin matsalar raunin azzakari kamar haka:

 

1. Motsa Jiki

“Akwai hanyoyi da waya da ake bi, don maganin raunin azzakari, amma motsa jiki na daya daga cikin mafiya shahara da saurin kawo fa’ida. Wani likita ya bayyana motsa jiki a matsayin hanyar mafi sauri da za a iya maganin raunin azzakari. Motsa jiki na sanya sassan jikin dan-adam su yi aikinsu yadda ya kamata, kuma ta haka ne, ya ke yaƙar matsalar raunin zakari.

 

Motsa jiki na inganta kewayawar jini a jikin mutum, wanda yake da matukar mahimmanci ga ƙarfin azzakari. Motsa jiki na inganta kewayawar jini ne ta hanyar haɓakar sanadarin ‘nitric oxide’ a cikin magudanar jini, wanda ya ce shine daidai yadda Viagra ke aiki..


Post a Comment

0 Comments