2⃣ bance ki auri wanda bashida sana’a koh aikin yi ba,mutukar yanada kwakkwarar sana’a ko aikin daxai iya rikeke,sannan kin yaba da halinsa mutumin kirki ne my dear kawai ki aure shi kawai arziki na Allah ne.
3⃣ kinga wannan dinner in anyi ma ‘yan kwanaki kadan bayan bikin an manta za’a barkine kije ke kada kiji da abinda kika aura in kinbi kyale kyalene ba kyan hali ba Allah kiyaye kwanaki kadanne an fara samun issues amman in kinbi hankaline da halin kirki toh ina miki albishir da.
4⃣ wannan time dinne zakisan kinyi aure kuma sbda zakuyi rayuwa me cike da farin ciki and marabar bawa da arziki mutuwa so ba namaki nan gaba shima Allah yayi mishi Arziki to ina me tabbatar miki sai kinfi kowace mace jindadi don yasan soyayyar tsakani da Allah kke msa bata kudi ba.
Menu
maijalalaini
Search for
Advertisement
Home/Magun Guna
Magun Guna
Kar kayan lefe da kyalekyalen bikin Aure su hanki auren mutumin kirki

Photo of Admin Admin6 hours ago0 166 6 minutes read
Kar kayan lefe da kyalekyalen bikin Aure su hanki auren mutumin kirki,
wata rana zakiyi dana sani.
Related Articles
KARFIN MAZAKUTA GA MAZA:
February 15, 2023
Innalillahi wa’inna Ilaiyi rajiun kalli yadda istim’nai yake illatar da mutum, hanyoyin da zaka dena aikawa
December 7, 2022
Muhimmancin Yarda Da Juna A Tsakanin Ma’aurata:
3 weeks ago
2⃣ bance ki auri wanda bashida sana’a koh aikin yi ba,mutukar yanada kwakkwarar sana’a ko aikin daxai iya rikeke,sannan kin yaba da halinsa mutumin kirki ne my dear kawai ki aure shi kawai arziki na Allah ne.
Advertisement
3⃣ kinga wannan dinner in anyi ma ‘yan kwanaki kadan bayan bikin an manta za’a barkine kije ke kada kiji da abinda kika aura in kinbi kyale kyalene ba kyan hali ba Allah kiyaye kwanaki kadanne an fara samun issues amman in kinbi hankaline da halin kirki toh ina miki albishir da.
Advertisement
4⃣ wannan time dinne zakisan kinyi aure kuma sbda zakuyi rayuwa me cike da farin ciki and marabar bawa da arziki mutuwa so ba namaki nan gaba shima Allah yayi mishi Arziki to ina me tabbatar miki sai kinfi kowace mace jindadi don yasan soyayyar tsakani da Allah kke msa bata kudi ba.
Zawarawa zasu kashewa yan mata kasuwa.
Wannan kam al’amari ne mai ban mamaki, kuma da yawa zasu iya cewa hakan ba zai yuwa ba. Amma idan kuka dubi hujjojin da zan kawo zaku gamsu da hakan. Yana da kyau me karatu ya fahimci cewa wannan prediction ne kawai. Wato hasashe ne duba da wasu al’qalma da suke gaba na kamar haka:
1. Tsadar kayan Lefe – Bayani daga bakin wanda su kayi aure a 2020 da kuma wanda ku kayi a 2022, ya nuna cewa a 2020 naira 500,000 zata iya maka kayan lefe na rufin asiri. Amma a shekarar 2022, naira million daya baza ta maka komai yadda kake so ba. Saboda yan mata sun saka buri akan lefe. Yanzu yar talaka ma so take kayi mata lefe akwati set uku zuwa abin da yayi sama da haka. Wannan yana nuna cewa nan da shekara biyar masu zuwa, samari baza su iya auren budurwa ba, saboda bukatun ta sun fi karfin talaka. A yau akan lefe sai a fasa aure, duk da cewa shi lefen mai kai 10 bisa 100 na abubuwan da mace zata samu a rayuwar ta ta aure ba. Sun gwammace su rasa miji da su yi hakuri da abinda namiji ya kawo.
Ita kuwa bazawara yanzu akwai su har da kanana. Sai kaga yarinya yar shekara 18, 19, 20, 23, fresh, tana neman miji. Kuma ita sadaki kawai take nema a wajen ka. Idan ka samu yar tarbiyya, wallahi ta fiye maka wannan marasa kunyan yaran masu burin bala’e.
2. Al’adun biki marasa asali – Bayan saurayi ya kai lefe an yi dace sun karba. Babban tashin hankalin sa kuma shine sai a fara jero wasu events, dinner, mothers eve, fathers eve, friends even, cocktail, gada party, waye party, duk gasu nan kalama. Kuma ace dole sai ayi wasu daga ciki. A yau mafi karancin abin da zaka iya kashewa a event shine million daya. Idan kuwa so kake a fita kunya, sai ka kashe million biyu da doriya. Kuma idan kace baza ka iya ba, sai ayi ta tsine maka, ana jin haushin ka. Wata ma daga nan zaku fara haurawa da iyayen ta. Shi yasa da anyi aure wata uku sai kaji anyi saki.
Ita kuwa bazawara, dama ita auren ne ya dame ta. Don haka bata bukatar wani event. Idan tayi tsamari tayi walima. Shikenan.
3. Tsirface-Tsirfacen Biki – Ban da lefe da al’adun banza sai kuma kaji yarinya ta fito da wasu tsirface tsirface na neman kudi. A bada kudin wannan, a bada kudin wancan, kaji abu kamar bazai kare ba. Tun kafin ka aure ta, ta fara nuna maka rashin imani da rashin tausayi. Kawai ita dai ka biya mata bukatar ta, ko mutuwa zakai don rashin kudi ita ba ruwan ta. Toh anan ma bazawara ba ruwan ta. Highest tace ka bata kudin gyaran jiki 30k. Shikenan. Sai aure.
4. Dogon buri – Yan matan yanzu buri ya musu yawa. Tun baka aure ta ba, ta fara gaya maka plan din ta na rayuwa. Including abin da take ci, abinda take sakawa, abinda bata so da sauran su. Da zarar ta shiga, toh abinda zatayi maka yafi haka. Ita kuwa bazawara dama ta riga ta shiga rayuwar aure, tasan banbanci tsakanin reality and gaibu. So she is ready to submit and live peacefully.
Conclusion
A karshe by the time da ka auri yarinya fresher, sai kaga tazo ta barka da bashi, ga kuma matsalolin ta. Kana fama da biyan bashi, kana fama da new demands. Don haka ina hango cewa idan mata da iyaye basu gyara wannan matsalolin ba, toh nan ba da dadewa ba, maza zasu fara hijira zuwa wajen auren zawarawa a auren fari. Don haka zawarawa sai ku karkade shimfidar ku ku jira, lokacin ku yazo, zaku fara cin kasuwar samari. Dama auran zawara babbar sunnah ce. Jiya wani abokina ya daura aure da bazawara kuma auren sa ne na farko.
(
Zawarawa zasu kashewa yan mata kasuwa.
~~~~

0 Comments