Sirrin Ma'aurata Dayakamata Samari Da Yam Mata Su Sani A Yanzu Saboda Amfanin Abun Kalli Wannan Bidiyon Zakaga Cikakken Bayani Akan Haka👇👇👇👇

 







Bayani ne mai nauyin gaske da kuma ke kunshe da dunqulallun bayanai masu mahimmanci. kamar yadda na alkawarta abaya zanyi!


Toh saide da farko zan fara da cewa; gaskiya idan kasan ko kinsan bakya iya tsayawa ku karanta dogon post a natse komi mahimmancinsa toh ina rokonka dakai gaba kurum, domin post din me tsayi ne kwarai, ahakan ma na takaita shine bakuma nason rabashi saboda hakan zai iya sa wani parts din ya zamo missing… saika karancesa zaka fahimcesa da kyau ….

Amma nayi BOLD HEADLINES da paragraph aciki da zaka iya fahimtar inda ka tsaya koda baka karancesa lokaci daya ba.


🌻🌻🌻


Hakika rayuwa da kuma zamani sun canza takai ga wasu abubuwan da ada ake lullu6esu ayau sun fito fili har sunfara zamowa bakomi ba. Da yawa mutane basu dauki tattaunawa game da irin wadannan ke6antattun al’amura na jima’i wani abu ba musamman atsakanin sa’oin juna, abokai ko kawaye maza da mata.


Mata basa jin kunya su zauna tsakaninsu ko wani group-group suna tattaunawa game da yadda mazajensu ke saduwa dasu, subahanallah. Haka ma cikin Mazan… duk da ansan wannan bai daga cikin tarbiya ta musu lunci.

Toh saide nisara yacimu da yaki kuma dama Annabi ya fadamana inde muka daukesu ababen koyi toh Koda zina suka dawo yi agefen titi muma ana nan wataran sai mun fara jaraba hakan……


::::::::::::::::::::::~~~~~●~~~~~::::::::::::::::::


SHIN TAYA SUKA CIMU DA YAKIN ??


Anci mu da yaki ne ta hanyar kafofin internet da social media dake yaďa batsa da alfasha barkatai a waya📲 da mutum zai hau internet ya danna ya shiga shafin da duk yakeso ya kalla ko takalli duk irin abunda takeso na jima’i da rashin kyautawa, wanda kaso mafi yawa sun bude ido dasu ayau har kuwa da masu aure cikin masu bibiyar irin wadannan shafuka wanda hakan ya canza tunanin alumma daga fuskantar gaskiya zuwa  karya.

Sannan kuma uwa uba ga group-group na batsa a social media da haka kurum yaro ko yarinya zasu zauna su tsara batsa zallah sui posting kaga wacce ko aure batai ba amma ta zage tana bayanin yadda ake kwanciya…

ko kuma bayani yadda kaza ya kasance tsakanin wane da budurwarsa wance haka kurum kirkirarrun labarai na banza da wofi da mutum me cikakken hankali bazai dauka ba…..


~~~~~~~~~~~~●●●~~~~~~~~~~~


Toh amma kasan dake kwakwalwa wawuyace, sannan wasu tunaninsu bai wuce saman gashin kansu… wadancan rubututtuka da suke karantawa tare da videos da suke kallah duk sai su aransu lallai fa hakan ce ta faru… don haka nima ya zanyi nai kaza dinnan ko kuwa in Mace ce ya akai mijina bai mun kaza dinnan gaskiya yana cutata kenan.


Wanda dalilin hakan kesa sakararru cikin Matasan mu su bazama neman maganin gaba batare dafa yaje wajen likita andubasa an tabbatar baida lfy ba! A’ah kurum shine tunda yaji anqaga labari kan abunda baya iyayi toh kurum ya lamincewa kansa dole yana da bukatar magani shima baida lfy…


Hakan yasa gashinan matasan mu shekara 20 zuwa 45 nata faman fankan-fankan suna shan magungunan hausa dana turawa alhalin lafiyarsu kalau, raina wuya sukai sukaje kaa adalilin kallo da karatun abubuwan da gidadancinsu ne ya kaisa garesu… karshe har shaye-shayen magungunan ya haddasa masa matsalar da ada bashi  da itan.

Sirrin Ma'aurata Dayakamata Samari Da Yam Mata Su Sani A Yanzu Saboda Amfanin Abun Kalli Wannan Bidiyon Zakaga Cikakken Bayani Akan Haka👇👇👇👇 

Post a Comment

0 Comments