AL-AJABI GIDAN MUTUWA A GARIN TADURGA TA KARAMAR HUKUMAR ZURU DAKE JIHAR KEBBI.

 AL-AJABI GIDAN MUTUWA A GARIN TADURGA TA KARAMAR HUKUMAR ZURU DAKE JIHAR KEBBI.









 AL-AJABI GIDAN MUTUWA A GARIN TADURGA TA KARAMAR HUKUMAR ZURU DAKE JIHAR KEBBI.


Wannan gidan da kuke gani a hoto, ana kiransa da gidan Mutuwa. Yana wani gari da ake kira "Tadurga acikin Jihar kebbi..


Mutanen garin basu san wanda ya gina gidan ba, hakazalika basusan wanda yake rayuwa a cikin gidan ba. Sannan idan dare yayi za'aga hasken wutan Nepa ta ko ina acikin gidan duk da cewa babu wata wayar wuta da ta sauka a cikin gidan, haka ma ba'ajin wata kara koda ta generator acikin gidan.


Abunda yafi bada tsoro shine, babu wata kofa ta shiga cikin gidan balantana Gaje, duka gidan yana kewaye ne da katanga.


A shekara 2012 wani matashi mai suna Dan Banga yayi yunkurin sanin menene yake rayuwa a cikin gidan, nan take yayi tsalle ya haura katangar gidan, daga lokacin ba'a sake ganinsa ba har yau.


Hakazalika, tsuntsaye 🐦 basu bin ta saman gidan. A shekara ta 2010 Hukumar sauka da tashi ta Jiragen sama ta Jihar kebbi mai suna "kebbi State aviation center" ta haramtawa Jirage bi ta saman gidan.


Idan kuka lura dakyau zakuga kayan tufafi an shanyasu, wadannan kayan suna canza kala lokaci bayan lokaci.


An tabbatar da cewa a shekara 2005 an hango wata mata mai dauke da juna biyu a gefen Window na gidan tana kuka fuskarta da jikinta duk Jini, daga karshe matar ta kulle Window din, tun daga ranar ba'asan yadda abun yakare ba.


Wannan labarin wani Film ne wanda Ni da ALI NUHU mukaso shiryawa tareda UMMI RAHAB sai dai kuma kash gashi tayi Aure sai shirin Film din ya fasu.


Mun tashi lafiya, da fatan kun nishadantu da labarin,

Post a Comment

0 Comments