Wata Dattijuwa ‘Yar Shekara 81 a Kano ta Samu Nasarar Sauke Kur’ani Mai Girma

Wata Dattijuwa ‘Yar Shekara 81 a Kano ta Samu Nasarar Sauke Kur’ani Mai Girma

$ads={1}















$ads={2}


Wata Dattijuwa ‘Yar Shekara 81 a Kano ta Samu Nasarar Sauke Kur’ani Mai GirmaWata Dattijuwa ‘Yar Shekara 81 a Kano ta Samu Nasarar Sauke Kur’ani Mai Girma.

Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Dattijuwar mai suna Hajiya Asma’u Jibril wacce daliba ce a makarantar Hajiya Baraka Islamiyya Bachirawa a karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano, ta kasance daya daga cikin daliban makarantar sha biyu da suka yi saukar Kur’ani a karshen makon nan.A hirarta da wakilin mu, Hajiya Asma’u ta bayyana kadan daga cikin abubuwan da suka taimaka mata wajen samun wannan nasara ta sauke Al’Kur’ani mai girma.

Acewar Dattijuwar, tun tana karama ta taso da sha’awar ta samu ilimi, kasancewar mahaifinta Malami ne, wannan ya sa ta ju tana da sha’awar ta gaje shi mahaifin na ta.

Mai girma Magajin Malam, Hakimin Ungogo, Alhaji Abdulkadir Ahmad Chedi, ya sawa daliban albarka, ya muma shawarci daliban makarantar da su cigaba da karatun Kur’anin da sauran litattafan addini da kuma kokarin kamanta aiki da su.

Post a Comment

0 Comments