Masu aiko da rahotanni daga jihar Kaduna sun ce "An tono gawar limamin Masallacin Juma'a na Rigasa tare da ɗansa Muhammad Zangina waɗanda suka rasu kimanin shekaru 7 da suka gabata
An tono su ne sakamakon hanyar mota express da ta biyo ta kan su wacce gwamnatin jihar Kaduna ke ginawa a unguwar Rigasa kuma bayan tono su da nufin sake musu Kabari sai aka ga tankar yanzu-yanzu aka fito dasu daga Makara za'a saka su Kabari don kuwa har ƙamshin Turaren da ake sawa gawa bai gushe daga jikinsu ba
Muna fatan Allah ya sa mu cika da imani
0 Comments