A sanarwa da kamfanin mai na kasa ya fitar ranar Laraba, kamfanin ya kara kudin litar mai daga naira N189 zuwa N537.
Wannan sauyi a farashin zai fara aiki ne daga ranar Laraba 31 ga watan Mayu, kamar yadda hukumar NNPCPL ta bayyana a wata takardar da ta fitar ranar Laraba.
Wannan kari ya zo ne kwanaki bayan da gwamnati ta bayyana cewa za ta kawo karshen tsarin tallafin man fetur.
Idan ba a manta ba a cikin jawabin shugaban kasa ranar rantsar dashi ta jaddada cewa gwamnatin sa za ta janye tallafin mai kwatakwata saboda tallafin kara wa masu karfi yaki yi talakawa kuma na dada fadawa cikin kangin tsananin talauci.
Kakakin kamfanin man, Garbadeen Mohammed ya ce kamfanin ta yi wannan kari ne domin ya yi daidai da abinda ake ciki a fadin kasa game da man fetur da cinikin sa.
Ko ina a fadin Najeriya, mai ya koma naira N537 kowacce lita a wasu wuraren ma, naira 540 ake saida litar mai.
0 Comments