Innalillah wa inna ilaihiraji’un kalli illar dorawa yara tallah maza kudai na lalata

 




Innalillah wa inna ilaihiraji’un kalli illar dorawa yara tallah maza kudai na lalata.


Sana’ar talla tana da illoli masu ɗunbun yawa ga rayuwar mata musamman wanda sunkai munzalin yin aure, A mafi akasarin garuruwan jihohin Arewacin Najeria, yana wuya kayi tafiyan minti guda baka ga ƴan mata suna talla ba; a bakin kasuwa ko makaranta,tasha ko masana’anta,wureren leburori ko kan titi,gidajen kallon kwallo ko sinima, ilin kwallo ko gidajen dambe, babu dare babu rana.


Babban abunda zai baka mamaki shine, yawancin abubuwan da suke sayarwa basa wuce abun Naira dubu daya ko dubu biyar, amma yarinya zata bar gidan iyayenta tun da safe har zuwa dare da sunan talla.


 Mafi muni shine, wasunsu har lunguna suna shiga da katti da sunan talla.Illolin sune; talla tana kawo fiyade har ta kai ga taɓa mutuncin ƴa’ƴa mata,talla tana hana ƴa’ƴa mata sallah a kan lokaci, talla tana hana ƴa’ƴa mata karutu (na addini ko boko), talla tana ɓata tarbiyyan ƴa’ƴa mata,talla tana saka ƴa’ƴa mata suna kamuwa da cututtuka masu hatsarin gaske. 


talla tana saka fitsara da rashin kunya ga ƴa’ƴa mata, talla tana saka rashin kamun kai da rashin sanin ciwon kai ga ƴa’ƴa mata. talla tana kaskantar da mace daga kima da daraja da aka san ƴa’ƴa mata suna da shi. 


Duk dacewa baduka akahadu akazama dayaba, saboda komai lalacewar zamani sai an samu nakirki acikinta Wasu daga ckinsu sunayin tallanne badan suna soba, saboda yazama dole agaresu bayanda suka iya, Ammadai dukda haka gyara kayanka bazai zamto sauke muraba ba.

Post a Comment

0 Comments