Duk Namijin da ya kalli wannan Videon sai ya rikice

 

*Fyade* dai na nufin aikata ko saduwa da mace ko namiji, ta amfani da hanyar karfi, ba tareda amincewar dayan bangare ba. Fyade yakan iya faruwa namiji ya yi wa mace, ko ita mace ta yi wa namiji, ko yanzu da zamani ya lalace, namiji ya yi wa namiji ko mace ta yi wa mace.




Ba shakka wannan mummunan aiki ne da ba addini ko al’ada da suka aminta da shi.




 




*NAU’UKAN FYADE*




 




Fyade yanada nau’ukansa kamar haka:




 




*Fyade na kai tsaye*. Wanda galibi yakan faru ne tsakanin mutane da wata kila ba su san da juna ba, haka kawai namiji zai ji ya kwadaitu da mace ko ita ta ji haka, sai fyaden ya auku.




 




*Fyade tsakanin masoya*. Wannan nau’in yana faruwa ne tsakanin masoya da suka shaku da juna, wata kila ma sukan sadu a tsakaninsu, amma kasancewar yanayi na ita ta hana shi ko shi ya hana ta sai fyade ya auku tsakaninsu.




 




*Fyade na abota ko shakuwa*. Wannan yakan faru ne tsakanin mutane da suke a unguwa daya, wata kila kan yanayi na shigar mace har ya sa a ji ana so a mata fyade kasancewar ana wuri daya ana kallon motsinta.




*ZAINUDDEEN ZAIN*




_DR. ZAIN_




 




Assalamu alaikum wa rahamatullahi ta’ala wa barakatuhu.




*Fyade tsakanin ma’aurata*. Wannan yakan faru ne tsakanin ma’aurata inda miji zai danne matarsa da karfi domin ya biya bukatarsa




 




*Fyade na taro*. Wanda aka fi sani da gang rape, shi wannan fyaden mutane da dama ne za su taru kan mace daya, ko wannensu ya yi amfani da ita, galibi irin wannan fyaden har rasa rayuwa ake yi.




 




*LAIFIN WA YE?*




 




Kai tsaye ba za mu iya ayyana wasu al’umma muce laifinsu ne ba kan fyade da ke faruwa, amma ba shakka faruwar fyade a cikin jama’a akwai laifi na:




 




*IYAYE*. Sau da yawa bahaushe kan ce, “sadaka daga gida takan fara” iyaye musamman mata, su tarbiyyar mata take a hannunsu, su ake tunani susan shiga da fita na ‘ya’yansu mata, saboda galibi yanzu fyade ya fi aukuwa kan mata ne. amma sai ka ga uwa yarinyarta budurwa ta fita tun safe ba za ta neme ta ba har dare lokacin yarinyar za ta dawo, ina taje, oho! a ina ta ci abinci, oho! wasu ma sai ka ga ba a gida suke kwana ba. A bangaren kananan yara kuwa, sai ka ga uwa ta bar yara kanani mata suna fita ba ko wando a jikinsu, a haka za su dinga gararanba kan titi da lunguna suna wasa cikin yara suna giftawa gaban miyagun unguwa, kafin uwa ta Ankara ankai ta anbaro, sai ta dawo dora hannu bisa kai, bayan tun farko laifinta ne. laifin uba anan shi ne, an ji ya fita aiki ko neman abinci, idan ya dawo me yasa ba ya bincikar wanne hali yaran nasa suke ciki? Ko ya dinga dan dawowa daga wurin aiki domin duba yanayin gidansa. Gaskiya ni a wurina laifin iyaye ne ta 98%.




Yara su ji tsoron Allah su dinga amfani da abinda ake karantar da su a islamiyya, su dinga shiga irin wacce musulunci ya tanadar.




 




A dinga yi wa mazaje aure idan aka lura ba za su iya kame kawunansu ba.




 




*ILLOLIN FYADE*




 




Daga cikin illolin fyade:




 




*KAMUWA DA CUTUTUKA*. Galibi masu yin fyade za ka tarar suna yin holewarsu a gefe, wasu ma sai a tarar suna dauke da miyagun cututuka irin HIV ko STDS. Sai kuga an sakawa wadanda aka yi wa fyaden ba su ji ba ba su gani ba. Hakan ta sha faruwa




 




*SAMUN RAUNI*. Ksancewar da karfi ne ake yi wa mace ko namiji, a yayin aikatawar wasu akan ji musu da rauni sosai, wasu a al’ura har jini ya dinga fita musamman yara kanana, wasu kuma a jikinsu ake ji musu da ciwon.




 




*RIKITA MUTUM DA FITAR DA SHI A HAYYACINSA*. Wasu da ake yi wa fyade, sai ka ga har abin ya taba kwakwalwarsu, wasu ma sukan sami tabin hankali da makamantansu.




 




*ZUBAR MUTUNCIN SHI WANDA YA AIKATA FYADEN*. Duk wanda aka ce ya taba yin fyade, za ku ga mutuncinsa ya ragu a idanun mutane zai zamo abin gudu kuma abin kyama, wanda har zuri’arsa ba za su tsallake abin fada ba kan fyaden.




 




*SHAFAWA WANDA TSAUTSAYIN YA FAR WA TABO*. Wasu suna rike mata da yawa da wannan tsautsayin ya far wa, bacin ba laifinsu ba ne, amma a haka wasu har ba’a ake musu, wasu kuma ana musu dariya da nuna musu kyama. Wanda sam bai dace ba.


*GWANNATI*. Dimokuradiyyance, an ce gwannati an kafa ta ne domin ta kare hakkin duk wani dan kasa nata, idan haka ne kuwa yanada kyawu a tarar a kowacce unguwa akwai tsaro daga gwannati ta yadda fyade zai ragu a cikin al’umma, amma gaba daya gwannati hankalinta ya karkata kan cika aljihunta da lasawa bakinta abu mai dadi, wanda ba karamar barazana ba ce a tsaro na kasa ma baki daya.




 




*YARAN DA AKE YI WA.* Wani/ta za su yi mamaki idan nace da laifin yaran da ake yi wa fyade, idan muka duba yanzu zamani ya yi lalacewar da wasu dunki da ake yi, gaba daya sai ka ga jikin mace ya bayyana kama daga nonuwanta har kira ta kunkurunta, wanda kai tsaye idan cikakken namiji ya kalla zai ji ya kwadaitu, hakan kan janyo fyade ya aiku. Wasu yaran sukan yaudari samari sosai, su kuwa samarin domin ramuwa kan yaudara da aka yi musu, sai ka ga sun yi wa yarinya fyade.


Yara su ji tsoron Allah su dinga amfani da abinda ake karantar da su a islamiyya, su dinga shiga irin wacce musulunci ya tanadar.




 




A dinga yi wa mazaje aure idan aka lura ba za su iya kame kawunansu ba.




 




*ILLOLIN FYADE*




 




Daga cikin illolin fyade:




 




*KAMUWA DA CUTUTUKA*. Galibi masu yin fyade za ka tarar suna yin holewarsu a gefe, wasu ma sai a tarar suna dauke da miyagun cututuka irin HIV ko STDS. Sai kuga an sakawa wadanda aka yi wa fyaden ba su ji ba ba su gani ba. Hakan ta sha faruwa




 




*SAMUN RAUNI*. Ksancewar da karfi ne ake yi wa mace ko namiji, a yayin aikatawar wasu akan ji musu da rauni sosai, wasu a al’ura har jini ya dinga fita musamman yara kanana, wasu kuma a jikinsu ake ji musu da ciwon.




 




*RIKITA MUTUM DA FITAR DA SHI A HAYYACINSA*. Wasu da ake yi wa fyade, sai ka ga har abin ya taba kwakwalwarsu, wasu ma sukan sami tabin hankali da makamantansu.




 




*ZUBAR MUTUNCIN SHI WANDA YA AIKATA FYADEN*. Duk wanda aka ce ya taba yin fyade, za ku ga mutuncinsa ya ragu a idanun mutane zai zamo abin gudu kuma abin kyama, wanda har zuri’arsa ba za su tsallake abin fada ba kan fyaden.




 




*SHAFAWA WANDA TSAUTSAYIN YA FAR WA TABO*. Wasu suna rike mata da yawa da wannan tsautsayin ya far wa, bacin ba laifinsu ba ne, amma a haka wasu har ba’a ake musu, wasu kuma ana musu dariya da nuna musu kyama. Wanda sam bai dace ba.




A nan ba wai ina maganar mace ko namiji ba. Saboda shi fyade har mace ma zata iya yi wa namiji.




Dan haka matsawar suka yawaita karanta batsa, ko kuma kallon batsa, a ko wane lokaci shaawarsu zata iya tashi, wadda zasu kasa controlling din kansu, a karshe su tari duk wanda Allah ya hada su da shi kawai su masa fyade.




 




Da saura da dama wanda lokaci ba zai bani damar bayyana su ba. Zan fada ga illolinsu kai tsaye.




 




Fyade yana da illoli da dama, daga cikinsu akwai;




 




1- Zubewar mutuncin mace ko namiji.




Daga sanda aka samu labarin an ma mutum fyade, mutuncinsa zai zube a idon jamaa, ba za a taba duba laifinsa ne ko kuma ba laifinsa ba? Idan namiji ne ma zai iya rasa matar aure, haka mace ma zata iya rasa mijin aure.




 




2- Bibiya




Idan aka miki fyade, wannan tabon zai ci gaba da bibiyarki har diyan diya, ana goranta masu, koda bayan bakya raye ne.




 




3- Rasa rayuwa




Mutum zai iya rasa rayuwarsa idan aka masa fyade, musamman ma ga kananan yara, wanda babu wani abu nasu da ya gama yin kwari.




4- kamuwar wata cuta




Idan wanda ya miki fyaden yana da wata cuta, babu wuya ke ma zaki kwashi wannan cutar.




 




Da sauransu.




 




Hanyoyin magance su:




 




1- gwamnati ta samarwa matasa aikin yi, su dogara da kansu, su samu su yi aure. Hanya ce babba wadda zata kawo warwara daga duniyar fyade.




 




2- iyaye su ringa suturta yaransu kanana. Idan suka ga yaransu yan mata zasu fita sunyi shigar banza, su dakatar da su daga fitar har sai sun saka kayan mutunci.




 




3- Mu marubuta mu gyara rubutunmu, mu ringa nusar da illar aikata fyade, mu tunatar da illolinsa. Sannan kuma mu daina saka batsa a labaranmu, shi kanshi zai iya bada nashi contribution din.




 




4- gwamnati ta ringa daukar tsatssauran hukunci ga duk wadda ko wanda aka kama da aikata fyade. Yanzu muna wani yanayi wanda cin hanci da rashawa ya yawiata, wai sai a kama mutum da laifin aikata fyade, amma da wuya ma ya kwana, sai ku ga an sake shi. Fi sabilillahi ba dole su ci gaba da yi ba?




 




A gurguje na yi duka bayanan, saboda bani da lokaci sosai ina karatun exam.




 




Allah ya bamu ladar.




 




*Saudat abdullahi (SAJ)*




A gaskiya wannan maidu’i yanada muhimmanci kwarai awannan zamani damuke ciki, musammsn in akayi la’akari da yadda yayi yawa yanzu,




 




Shidai wannan kalma ta FYADE yana nufin cin zarafin y’a mace ko keta haddin ta, batareda bisa shari’aba ko yardanta ba .




Aikata fyade yazama ruwandare awannan zamani namu, samarine, tsofaffine, yan siyasane, zuwa masu kudin kasannan, duk aikin dasuke aikatawa kenan wa’iyazu billah,




 




DALILAN DAKE KAWO FYADE.




 




Matasanmu kan afka wannan mugun aikine sabida dalilai Kamar haka




1,kallon finafinan batsa da turawa suka shigo mana dashi, dazaran yara sunkalli yadda ake kwanciya da mace, to sai sha’awarsu ta motsa, mezaifaru sai nemsn yadda zasuyi su gusarda sha’awar tasu, wato sukwanta da yarinya kota halin kaka.




2, influence na peer group, dasuke jan ra’ayinsu suyi kungiya su aikata hakan sakamakon sunkai munzalin aikatawar.kuma babu halin aure alokacin.




3, Shigar banza da y’an matan zamani keyi , saikaga yarinya tayi dinki daya bayyana surarta afili, ga nonuwa awaje, sannan babu hijabi sai guntun gyale mai nuna surar jiki,sun wuce samari suna kada jiki dole sutada musu shaawa daganan sai mai aukuwa ta auku, bayaga musulunci takoya mana duk wani nau’i na rayiwa dazamuyi, shiyasa akace “,AL MAR’ATU KULLUHA AURATUN ILLA WAJAHAHA WA KAFFAIHA,”mace duk cikanta al’aurace in banda fuskarta da tagukkanta, meyasa akace haka? Sabida gujewa afkawa iron wannan mugun aiki.




Sai kuma karancin ilimin addini/tarbiyya , wasu yaran basu dace da iyaye da sukasan hakkin y’ay’ansu akansuba, basu damuda ilmantardasu addiniba balle tarbiyarsu, saikaga iyaye basuma San inda yarabsu sukeba ko irin abokananda suke hulda dasu.




Tsofaffi kansu sukan afka cikin wannan mugun aiki, wanda zan iya siffantashi da raunin imani, nashajin labarin tsoho ya lalata yarinya mai kankanin shekaru 4, 9,da sauransu , Allah kasa muyi kyakyawan karshe,




Yansiyasa suma baa barsu bayaba wajen wannan mugun aiki, domin neman matsayi ko cimma wasu buri nasu saikaga suna aikata shi,




Haka zalika masu kudi suma sana’ar kenan, domin bokansu yatabbatar musu sai sunyi hakan zasu sami arziki, wasuma har mahaukata suna kwana dasu, kama har y’anuwansu na jini.




 




MAFITA




 




Toh nidai aganina babban mafita shine addu’a mudage da addu’a domin Allah samiu dua’a ne, sannan mu kyautata tarbiyyar yaranmu domin abin tambaya ne gobe kiyama agaremu, daga mazan har matan kuwa,murage son abin duniya dawani dogon buri, rayuwa mai karewane, canne wajen tabbata.




Allah yakara mana zuri’a yashiryaddasu shirin addinin muslunci,




Masu wannan hali kuma Allah yashiryesu yasa sugane gaskiya su daina.




*Aisha Nasir kiru(maman imaam)*




 




Agaski wan nan babbar mastalace ta fyade musamman ga kana nan yara, munsha samun matsalar a asibi angawosu tare da police domin duba IYA barnan da akayiwa yarinyar, wlh watama mutuwa tayi, kuma acikin unguwa abin yafaru, wlh bawani mataki da akadauka akai, kuma ba laifin mamanta ciki, Allah ne yakawo wan nan kaddar, amma wasu kuma gaskiya sakacine Dan basaneman yaransu saizasuyimusu aike,ko kuma dare yayi basudawoba,alokacinne za atuna aibasa gida, don Allah iyaye mukula da amanar da Allah yabamu domin zaitambayemu idan kiyama tatsaya, Allah yatsaremu dafadawa akan wan nan kaddarar Amin👏👏👏




 




*Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuhu.*




 




*AISHAN UMMA*




 




*Fyad’e*




Yana nufin tilastawa ga mace ayi amfani da ita ta k’arfin tsiya, ko kuma yiwa k’ananan yara wayo ta hanyar basu alawa subi mutum d’aki ya danne su ba tare da tsoron Allah ba, ko kuwa a samu jaririya k’aton saurayi ko sa’an kakanta ya aikata mata yayi mata illa, wadda shi fyad’e yana kaiwa wani lokacin har mace ta rasa ranta walau babba ko yarinya.




 




*Matsalar fyad’e*




Tana farawa ne daga lokacin da uwa ta haifi d’iyarta harya kasance sam bata saka ido akanta, kowa yana da damar d’aukarta ya fita da ita, wannan babban k’alubale ne, musamman da yanzu tsoron Allah yayi k’aranci, wani ubanma shi kewa ‘yarsa balle kuma ace k’aninsa ko almajirin gida ko kuwa ‘yayan mak’ota. Idan aka wuce matsalar a b’angaren jarirai akazo kan yaran da suka fara fita, shima rashin saka ido da killace yarinya da suturta yana taka muhimmiyar rawa gurin lalata tarbiyyar yarinya, idan har yarinyarki tayi wayon da zaki aiketa ko ta fara zuwa makaranta, yana da kyau kijata a jikinki kuma ki dinga killaceta ki nuna mata karta yarda ko da wasa wani ya rik’e mata koda hannu ta hanyar tsoratarwa da ze iya kasheta da makamantansu, to wani lokacin sam iyaye babu ruwansu da lura da ‘ya’yan nasu sun fita a nemesu, harse sun dawo dan kansu, kuma koda taganta da abinda ba ita ta bata ba, ba lallaine ta tambaya ba. Matsala kuma ta yiwa ‘yan mata yana farawa ne daga shiga ta fidda tsiraici da sukeyi, shiga mara kamala ko wace sura a waje, wannanma yana kawo yawaitar fyad’e duk da cewa wata kuma k’addarace ta saukar mata amma kashi 90 ya danganta da yanayin shigar su, wasu kuma rashin kunya ke jawo musu, mace ta cika tsiya kowa ta tsaya tace zatai masa rashin mutunci ita ta isa, to wani seya k’ullata daman ya saba yace seya fanshe anan.




*Mafita*




Mafita ta farko itace addu’a ki kasance a matsayinki na uwa kina yiwa yaranki addu’a daga dukkan sharri mazansu da matansu, ki dinga karanta musu addu’ar da Annabi sallalahu alaihi wa sallam ya kewa su Hussain “u’izukuma bi kalimatillahi tammat, min kulli shad’anin wa hamma wa min kulli ainin lamma.” Se kuma ki rok’i Allah ya taimaka miki akan tarbiyyarsu, kuma kici gaba da basu tarbiyya da kulawa kina had’awa da addu’a, ki kula da yaranki karki dinga barinsu sakaka, ko yaya kike da namiji karki dinga bari yanai miki nisa da ‘ya’ya, kuma karki lamunci wasan banza, karki kuskura ki dinga barin yaranki tsirara walau mace ko namiji. Ga ‘yan mata kuma a dinga suturce jiki ana shiga ta kamala, indai ko wace mace zata kasance kamila me suturce jikinta kuma ba ballagaza ba to babu shakka da yardar Allah abin ze ragu, maza kuma suji tsoron Allah! Dan wani ba zaka ce ba a bashi tarbiyyaba iyayensa sunyi k’ok’ari amma seka rasa daga ina suka gurb’ata tarbiyyar, sam babu imani da tsoron Allah a tattare da wanda ze turmushe jinjirar ‘ya da bata ma san meke cikin duniyar ba.




 




*Illolin fyad’e a al’umma*




Suna da matuk’ar yawa, a ciki akwai rashin rayuka da ake samu na kanan yara harma da ‘yan mata da matan aure. Akwai yad’uwar karuwanci a al’umma, ma’ana wata da zarar anyi mata fyad’e ta warke se kuma taji ba zata iya zama haka ba se tayi mu’amala da namiji, akwai yad’uwar cututtuka harda me karya garkuwar jiki, sannan kuma zakaga babbar illar shine rashin yin hukunci ga wanda ya aikata hakan koda kuwa an kamashi se a sakeshi musamman idan d’an masu hali ne.




 




SHARHI DAGA *SIRRIN RIKE MIJI*




 




gaskiya an taba komai cikin wannan topic din na fyade, kuma yana DA kyau al’ummar mu su maida hankali kan kula DA ya’yan su da duk karfin ikkon su, Allah ya bamu iko amin.

Post a Comment

0 Comments