Babban Sifeton ƴan sandan kasar nan Usman Alƙali Baba ya kori jami’an ƴan sanda uku da ke yiwa fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara rakiya.

Babban Sifeton ƴan sandan kasar nan Usman Alƙali Baba ya kori jami’an ƴan sanda uku da ke yiwa fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara rakiya.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar Olumuyiwa Adejobi ya fitar, yace an kori ƴan sandan ne sakamakon kama su da laifin harbin iska, ba tare da dalili ba.

Ƴan sandan sun yi harbi a sama lokacin da Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gama rabon tallafi zai shiga motarsa, wanda rundunar tace hakan ya saɓawa dokar rundunar.

Post a Comment

0 Comments