Kwankwaso, Kwankwasiyya Da Yankan Kunkurun Bamaguje A 2023, Daga Mamman Ɗan Mamman

Babbar matsalar da siyasar Kwankwaso ke fuskanta, ita ce ta tawaye ko barambaram da tunanin sa ya yi da maganar nan da ake cewa, “ɗan Adam ba zai taɓa halaka ba, matuƙar ya san kan sa.”

Matsalar sa ita ce, ƙoƙarin da ya ke na ya zama abin da bai gama fahimta ba. A tunanin sa, a yau shi ne Malam Aminu Kanon wannan zamani. Sai dai bisa ga dukkan alamu, bai ma fahimci me Malam Aminu Kano ya rayu ya kuma mutu a kai ba. Kusan a iya cewa, ya yi wa abin ba wan ba ƙanin – karatun ɗankama. Domin kuwa, a haƙiƙanin gaskiya, da alama tun a babbaƙu ma aka jefara shi.

Ba zan ɓata lokaci a kan mene ne tunani da aƙida irin ta Malam Aminu ba, domin hakan zai iya ɗaukar mu wani dogon lokaci kafin mu gama. Amma zan mayar da himma ne a kan mummunar fahimtar da mutane ke yi wa tunani da aƙidar siyasa irin ta Malam.

Ɗaya daga cikin dalilan haɗa Kwankwaso da Malam Aminu shi ne, ɗaya daga cikin abubuwan da Kwankwaso ya fi bai wa muhimmanci shi ne, sanya jar hula kamar yadda Malam Aminu Kano shi ma a iya rayuwar sa yake sanya jar dara.

Sai dai ya manta, hakan ba ta taɓa zama wata alama ta mabiya Malam Aminu ba. A haƙiƙanin gaskiya ma, an fi kwaikwayon sanya sutura irin ta Rimi da ta Shagari a wannan zamani fiye da irin shigar Malam Aminu Kano.

Premium Times Hausa
Kwankwaso, Kwankwasiyya Da Yankan Kunkurun Bamaguje A 2023, Daga Mamman Ɗan Mamman
Premium Times HausabyPremium Times Hausa March 10, 2023
2023: Ko matasa da talakawa za su yi wa Kwankwaso halasci su taya shi kayar da ‘gwankin’ Arewa da ‘giwar’ kudu?
Babbar matsalar da siyasar Kwankwaso ke fuskanta, ita ce ta tawaye ko barambaram da tunanin sa ya yi da maganar nan da ake cewa, “ɗan Adam ba zai taɓa halaka ba, matuƙar ya san kan sa.”

Matsalar sa ita ce, ƙoƙarin da ya ke na ya zama abin da bai gama fahimta ba. A tunanin sa, a yau shi ne Malam Aminu Kanon wannan zamani. Sai dai bisa ga dukkan alamu, bai ma fahimci me Malam Aminu Kano ya rayu ya kuma mutu a kai ba. Kusan a iya cewa, ya yi wa abin ba wan ba ƙanin – karatun ɗankama. Domin kuwa, a haƙiƙanin gaskiya, da alama tun a babbaƙu ma aka jefara shi.

Ba zan ɓata lokaci a kan mene ne tunani da aƙida irin ta Malam Aminu ba, domin hakan zai iya ɗaukar mu wani dogon lokaci kafin mu gama. Amma zan mayar da himma ne a kan mummunar fahimtar da mutane ke yi wa tunani da aƙidar siyasa irin ta Malam.

Ɗaya daga cikin dalilan haɗa Kwankwaso da Malam Aminu shi ne, ɗaya daga cikin abubuwan da Kwankwaso ya fi bai wa muhimmanci shi ne, sanya jar hula kamar yadda Malam Aminu Kano shi ma a iya rayuwar sa yake sanya jar dara.

Sai dai ya manta, hakan ba ta taɓa zama wata alama ta mabiya Malam Aminu ba. A haƙiƙanin gaskiya ma, an fi kwaikwayon sanya sutura irin ta Rimi da ta Shagari a wannan zamani fiye da irin shigar Malam Aminu Kano.

Ba a nan kaɗai ta tsaya ba, wani tunani na Kwankwaso a kan Malam Aminu shi ne, ganin da ake siyasar Malam Aminu siyasa ce ta fitsara da tawaye ga magabata. Ko shakka babu, a wasu shekaru da su ka gabata, salon siyasar Malam Aminu Kano kenan, wanda har hakan ta sanya, Sarkin Kano Bayero ya taɓa ce masa “Malam Aminu ba ka ganin wata rana wannan abin da ku ka koya wa yara, zai fi ƙarfin ku?” Hakan kuwa ya faru, domin dawowa daga rakiyar irin waccan fahimta ta siyasa da Malam Aminu Kano ya yi, a zamanin da ya kafa jam’iyyar PRP, shi ne maƙasudin da ya janyo rikicin sa da Gwamnan Kano na wancan lokacin, marigayi Abubakar Rimi.

Sakamakon hakan ne ma ya janyo darewar jam’iyyar ta PRP, tsakanin Santsi da Taɓo. Wannan rikici ne ya janyo har Gwamna Rimi ya yi wata lacca da ya yi wa mutuncin Malam Aminu Kano hawan-ƙawarar da sai da Malam ɗin ya rubuta a wani kundin sa, “Ko shakka babu Rimi maƙiyi na ne.”

Idan muka yi la’akari da wannan, za mu iya hasashen irin haɗarin da Kwankwaso ke neman jefa kan sa, da kuma siyasar sa. Domin dai shi kan sa wanda ya ke ganin shi ya ke kwaikwayo, bai gama da aƙidar lafiya ba. Ta kai ga yaran da suka koya wa raini da cin zarafin magabata, da suka gama cin zarafin mutanen, sai suka koma kan su. To haka shi ma Kwankwaso, waɗannan yaran da yake nuna wa ba wanda ya isa sai shi, ranar da duk suka rasa wanda za su yi wa fitsara, kan sa za su dawo.

Wata babbar masifar da kuma sabon salon da Kwankwaso da Kwankwasiyya ke ƙoƙarin ɗora matasa a kai, ita ce siyasar daba da zubar da jini a Kano. Ko shakka babu, tarihi ya tabbatar da cewa, siyasar daba ta fara shigowa Kano ne, a zamanin NEPU, sakamakon halin da mabiyan ta suka tsinci kan su na rashin tsaro ga tarukkan su da su kan su ma. To amma hakan ba ta taɓa haifar wa Kano ɗa mai ido ba.

Daga irin kalaman da ke fitowa daga bakunan shi jagoran na Kwankwasiyya, da kuma wasu mabiyan sa, za ka tabbatar da cewa Kano na cikin wani garari, musamman a zaɓen gwamna.

A lokacin da ya shigo Kano, makonni biyu da suka gabata, Kwankwaso ya yi iƙirarin cewa, zai iya sanya mabiyan sa su shiga su ɗauko gwamna su cinye shi kamar karas. Wannan ba ƙaramin tunzura matasa ba ne. Domin ko ba komai, shi da yake maganar ya taɓa zama gwamna, ya kuma san illar da za ta biyo baya idan har hakan ta fara. Domin za a sanya Kano a cikin wani mummunan hali na rashin doka da oda, kuma shi kan sa ya san cewa, hukuma ba za ta yi masa da wasa ba, matukar hakan ta faru.

Wata babbar masifar da shi da kan sa ya ke iƙirari ita ce, batun da yake ta yayatawa na cewa, idan har Abba ya ci zaɓe, da kan sa zai hau katafila ya rushe dukkan wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnati. Sai dai ya manta da cewa, ko da Abba ya ci zaɓe, shi fa ba shi da wani muƙami da zai ba shi dama ya aikata haka.

Hukuma ce kawai ke da wannan ƙarfi, a kuma hukumance babu muƙamin ka-fi-gwamna. Yin hakan zai iya janyo rikicin da zai iya jefa Kano da tattalin arzikin ta cikin wani mummunan hali.

Irin waɗannan kalamai da ke fitowa daga bakin sa, su suka bai wa mabiyan sa ƙwarin guiwar, ɗaukar aniyar idan dai ba su suka ci zaɓe ba, to kuwa sai dai a fasa kowa ya rasa. Ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ‘yan majalisar tarayya da aka zaɓa daga Karamar Hukumar Kiru da Bebeji, wato Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya sa yake cewa, “Duk wani jami’in zaɓe da muka kama yana neman ya yi mana maguɗi, to za a ga shigar sa Bebeji, amma ba za a ga fitar sa ba.” Hakan na nuni da shirin mabiya Kwankwasiyyar na su ɗauki doka a hannun su. Idan kuwa har hukuma ta zura ido, hakan ta faru, kuma hukuma ta zura ido, to kuwa an ɗra ƙasar nan a kan wani tsari mafi muni, wanda zai iya jefa ƙasar nan cikin mummunan hali.

Allah ya kyauta mana!

Post a Comment

0 Comments