Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’un Cikakken Bidiyon yadda Akai Jana’izar Dan Sani Abacha Wanda ya Rasu Yanzu…












Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’un Cikakken Bidiyon yadda Akai Jana’izar Dan Sani Abacha Wanda ya Rasu Yanzu Ɗan Sani Abacha ya rasu Allah Yajikan Musulmi Ameen.


Abdullahi Abacha, wanda shi ne ɗa na biyun-ƙarshe ga marigayi tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya , Sani Abacha, ya rasu yana da shekaru 36 a duniya.


Iyalin Abacha suka tabbatar wa majiyar DCL Hausa ta DAILY NIGERIAN rasuwar a yau Asabar, inda suka ce Abdullahi ya rasu ne cikin barci a a gidansu da ke titin Nelson Mandela a Abuja.


“A daren jiya ma lafiya kalau ya kwanta, amma yau da safe sai gawarsa a ka samu. Ya rasu cikin kwanciyar hankali a cikin barcinsa,” in ji wata majiya daga iyalin Abacha.


Jaridar ta DAILY NIGERIAN ta ce za’ayi jana’izarsa da misalin karfe 4 na yamma a babban masallacin kasa da ke Abuja a yau Asabar.


                 Kalli cikakken video 👇












An haife shi a shekarar 1987, marigayin yana daya daga cikin yara tara da marigayi shugaban soji ya bari.

Post a Comment

0 Comments