Ummi Rahab da Mijinta sun taka sahun barawo akan abunda yake faruwa da Adam A Zango

 


A satin daya gabata ne fitaccen mawaki kuma jarumi a masana’antar kannywood Adam A Zango ya bayyanawa duniya halin da yake ciki dashi da iyalin shi.

Tun bayan fadin lamarin ne wasu suke ganin rashin kyautawar sa bayan ya fito ya fadawa duniya,wasu suna ganin sirrin sa ne ya kamata ace iya shi kadai ya san abunda yake faruwa a gidan sa sai kuma makusantan sa.


Amma jarumin daga baya ya goge fefen bidiyon daya saki yayi wannan bayanin kana ya kara bayyana dalilin sa na bayyanawa duniya.


Adamu Zango din yace “An jima ana jifana da kalaman rashin rike Aure na ko kuma auri saki,wanda ban taba tankawa ba, saboda mai daki shi yasan inda yake masa yoyo”

Jarumin sa’annan ya kara da fadin yana ganin daga Matar tashi Safiyat Chalawa ya gama Aure,saboda shi haka kaddarar tasa tazo.


Ana cikin hakan ne,sai aka ga wata wallafa a shafin Lilin Baba yana fadin “Mun godewa Allah matata ta tsallake Rijiya da baya”


Bayan wallafar ne kuma mutane suka dinga rura wuta ana cewa da Adamu Zango yake,amma daga karshe ya fita yayi bayani yace ba dashi yake ba,Ummi Rahab dince ta tsallake Rijiya da baya daga gurin wasu Ƴan damfara.

Sai dai tsagin mutane da dama sun bayyana babu kokonta da Adam Zango yake.


Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa,Kada ku manta kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!



Post a Comment

0 Comments