Duk da hukuncin kotun koli - wasu bankuna sun daina karbar tsaffin kudi a Nijeriya






Duk da hukuncin kotun koli - wasu bankuna sun daina karbar tsaffin kudi a Nijeriya


Wannan yanayi ya jefa yan Nijeriya cikin tsaka mai wuya matuka


Daga, Ibrahim M Bawa


Wasu bankuna da dama a cikin kasar nan, tun a jiya Litinin sun daina karbar tsaffin kudi a hannun kwastomominsu da suka kawo don shigar da su a bankunan, duk da kuwa hukuncin da Kotun Kolin Nijeriya ta yi na cewa a ci gaba da amsar tsaffin kudaden har zuwa ranar 15 ga watan nan na Febrairun 2023, da za ta yi hukunci na karshe kan a ci gaba da amfani da tsaffin kudaden ko a'a.


Za a iya tuna cewa gwamnoni uku ne suka shigar da karar a gaban kotun Kolin da suka hada da gwamnan jihar Kaduna da na Zamfara da kuma gwamnan jihar Kogi, inda suke rokon kotun Kolin da ta hana dokar haramta amfani da tsaffin kudaden N200 da N500 da kuma N1000 da CBN ta yi sakamakon kirkiro sabbin kudaden.


Sai dai tun kafin wa'adin ya cika a gobe Laraba, wasu bankunan tun a ranar Litinin sun daina amsar tsaffin kudaden da aka kawo masu don shigarwa, kamar yadda majiyar Katsina Daily News ta Daily Trust da BBC suka rawaito mana.


Wannan yanayin dai da aka shiga ya jefa yan Nijeriya da dama cikin tsomomuwar rayuwa, inda wasu da dama suka bayyana cewa sun kwana da yunwa sakamakon kin amsar tsaffin kudaden nasu wajen yan kasuwa da kuma bankuna.


A gobe Laraba ne dai kotun Kolin Nijeriya za ta yi hukunci na karshe kan batun za a ci gaba da amfani da tsaffin kudaden ko kuma sun haramta a daina amfani da s u kwatakwata.

Post a Comment

0 Comments