Abubuwan da Majalisar ƙasa ta buƙaci CBN ya yi kan matsalar sauya fasalin takardun Naira







Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.


Sa'o'i 2 da suka wuce

Majalisar magabata ta kasa a Najeriya wato Council of State, ta kammala wani taron gaggawa a fadar shugaban kasar da ke Abuja inda ta bukaci babban bankin kasar, CBN ya samar da karin sababbin takardun kudi domin amfanin al'ummar kasar.


A cewar majalisar, idan sababbin kudin ba za su samu ba, to CBN ya koma bai wa jama'a tsofafun takardun kudin.


Majalisar - wadda ke karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari - ta kira taron ne domin tattaunawa ka halin da kasar ke ciki a yanzu da ta ke tunkarar babban zabe.


Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin majalisar dattawa da na wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnon in kasar.

Ta kuma ce duk da matsalolin da ake fuskanta, tana goyon bayan tsarin babban bankin na sake fasalin naira.


Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku wanda ya yi wa manema labarai karin bayani ya ce, "An shawarci CBN ya samar da kudi ga jama'a sannan kuma a sake fito da tsofaffin kudi domin kawo karshen wahalar da jama'a ke fuskanta."


A waje daya kuma shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC Mahmood Yakubu, ya yi wa majalisar bayanai game da shirye-shiryen babban zaben kasar inda ya nuna cewa hukumar ta kammala shirin gudanar da zabukan da za a yi daga karshen wannan watan.


Shi ma babban sufeto-janar na 'yan sandan kasar Usman Alkali, ya yi wa majalisar bayanai game da irin matakan tsaro da suke shirin dauka a lokacin zaben.... 


Post a Comment

0 Comments