Mutuwar Kamal Aboki: Malam Ya Bayyana Darasi Ga Matasan Masuyin Abun Dariya (Comedy)

 Mutuwar Kamal Aboki: Malam Ya Bayyana Darasi Ga Matasan Masuyin Abun Dariya (Comedy).





Kamar Yadda Kuka Sani Dai A Jiya litinin Muka Samu Wani Labari Marar Dadi Daya Dauki Hankalin Mutane Sosai A Kafar Sadarwa, Shine Na Mutuwar Wani Jarumin Barkwanci A Masana’antar Kannywood Kamal Aboki.

Kamal Aboki Matashin Jarumine A Masana’antar Kannywood, Wanda Ya Kware Waje Hada Bidiyon Barkwanci Ko Kuma Muce Ban Dariya Wato (Comedy) Yana Wallafawa A Kafar Sadarwa Domin Mabiyansa Da Masoyansa.

Matashin Dai Ya Samu Lambar Yabo Akan Bidiyon Dayake Shiryawa Na Bandariya Da Abokan Aikinsa, Yadda Har Wasu Lokutan Yakan Shirya Wasu Gajerun Bidiyo A Shafinsa Na Instagram Da TikTok Yana Tambayar Mutane Akan Wasu Abubuwa Dasuka Shafin Sha’anin Addinin Musulunci, Wanda A Hausance Ake Kira Da Muhawara.

Muna Fatan Allah Yajikansa Ya Gafarta Masa.

Sai Dai Lamarin Daya Janyo Hankalin Wasu Mutane A Kafar Sadarwa Shine, Ansamu Wani Faifan Bidiyo Na Wani Malami Dayakeyin Live A Shafin TikTok Yana Mai Bayyana Cewa, “Annabi Muhammad Bayason Mutumin Dayake Kirkirar Abun Karya Domin Mutane Suyi Dariya”.

Wannan Yazo Dai Dai Lokacin Mutuwar Kamal Aboki Wanda Rohotanni Suka Bayyana Cewa Yayi Hatsarin Mota Ya Rasu A Hanyarshi Ta Dawowa Daga Nijar Zuwa Kano.

Ga Bidiyon Malamin Sai Ku Kalla Kuji Cikakken Bayani Daga Bakinsa:

To Allah Ya Kyauta Zamuso Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Bidiyo, Kuma Muna Mika Ta’aziyarmu Ga Iyalan Kamal Aboki Allah Yajikansa Da Rahama Yasa Mutuwa Hutuce A Gareshi Ameen.

A Wani Bangaren Kuma
CUTAR DUNDUMI KO GANIN HAZO-HAZO
______________________________________

Cutar dundumi ɗaya ce daga cikin larurorin dakan shafi idanu. Wannan larura ce ta dakushewar kaifi/ƙarfin gani, yanda mutum shi akaran kansa ke tabbatarwa da kansa yana da larurar domin baya bukatar zuwa wajen likita yin gwaji kafin ganota.

Masu wannan larurar galibi in sun zo wajen likita sukan ce likita gani na baida kyau, idona ina jin kamar an zubamin mai acikin sa, dususu nake ganin abubuwa ba irin tar-tar ba kamar da. Bawai duhu mutum yake gani ba…. a’ah yana ganin komi fes saide ba tar ba, abubuwa musamman manya kamar Motoci, gini, ko wani symbol duk yana ganinsu normal, amma kuma bai iya ganin rubutun jikin symbol ɗin fes-fes musamman in ƙanana ne bazasu karantu da kyau ba, zai iya ganin sun harhaɗe musamman in kwai yar tazara.

Wani lokacin sukan gani da kyau idan rana ta take, toh amma in yamma tayi musamman gefin magriba duhun nan nasa ganin nasu yai dususu sosai har sai daren ya taho anyi sallar magariba sai kyawun ganin nasu ya qaru. Wanda ke da wannan larurar nasan zaifi fahimtar me nake bayani da kyau.

______________________________________

Jiya nasa wasu hotuna inda nake tambayar tsakanin “A” da “B” wanne yafi fita fes? Inda dukkan masu gaskiya batare da son raurawar zuciya ba suka tabbar da hoton “A” yafi “B” fita, wanda tabbas hakan ne, ai baka bukatar ma yin wani tunani abu ne a fili, kai da gani kasani.

Don haka wanda suka zaɓi “B” bamu san meke damun idonsu ba, ƙila ko don ni nace “B” shiyasa suka zaɓi su bar gaskiya su ma su rufta rami 😊

Nayi wannan tambayar ajiya ne kafin kawo wannan karatun don kowa ya fahimta. Sashin ‘A’ ɗin shine yadda mutane masu “Normal vision” wato kaifin gani ke kallon abubuwa, yayin da shi kuma “B” ɗin tamkar hakane masu larurar dundumi ko gani hazo-hazo (blurry vision) ke ganin abubuwa, wato ga abin a haskake saide ba fes ba kamar de hotunan jiya da kuma na qasa jikin hoton ƙasan post dinnan.

______________________________________

Ita wannan larura ta rarrabu zuwa muhimman gidaje guda biyu;

1- Mai ganin hazo-hazo, dundumi-dundumi ko garara-garara daga nesa, wato “Short ko Near sighted” a turance, ko ince MAYOFIYA a yaren likitanci (myopia). da kuma

2. Mai ganin hazo-hazo, dundumi-dundumi ko garara-garara daga kusa, wato “Long ko Far sighted” a turance, ko ace HAIFAROFIYA a yaren likitanci (Hyperopia).

Dukkan biyu dinnan abu iri guda idanunsu ke nuna musu. saide

_____________________________________

MAYOFIYA: Masu wannan su suna iya ganin duk abinda yake kusa dasu fes wanda nisan sa dashi bai wuce taku goma ba “10feet”, yana iya karatu da rubutu normal. Inda matsalarsu take kurum in suka kallo abinda ke nesa sai suga baya fita sosai, ko fuskar mutum ce basa iya ganinsa fes sai ya matso kusa, haka ko TV suke kallo saide su zauna agaba kamar de yadda hotunan nan suka nuna. Yayin da shi kuma me

HAIFAROFIYA: suna iya ganin duk abinda ke nesa fes-fes kamar wata daren 14, amma kuma in abun kusa kusa dasu yake dab’ basa iya gani da kyau. Wato a me wannan matsalar shi abinda ke nesa kurum yake iya gani da kyau. Wadannan sunfi shan wuya wajen karatu a littafi ko sarrafa wayoyin hannu domin Baƙaƙen har haɗe musu suke, kaga mutum nata takure ido, har idanu suke zafi.

Abu ne mai sauƙi, ana zuwa aka auna idon mutum da karfin ganin nasa shikenan sai a yanka masa glass dede dashi… An warware matsalar angama. Domin karka dauka duk masu sanya medicated glass iri guda ne, a’a ba haka bane. Kowa karfin ganinsa daban, wani ma baya bukatar glass se zai karatu ko tuƙi.

Haka karka dauka me sanya glass makaho ne 😅 kurum refrective error ne inya sanya wannan glass din ya fika gani da kyau kai wanda bakasa glass din. Ko tsoho karka kuskura ka raina sa ganin yana sa glass kace zakai masa wayau kar yake kallonka, saide kai nasara ba akan baya gani ba, a’a sai akan kwakwalwarsa baya iya tuna abubuwa saboda tsufa.

______________________________________

Wanda kuma basason sanya glass akwai Contact lenses shima kamar glass sai an auna idon, wanda da yawa har celebrities sun fi ga contact lenses tunda shi acikin idon za’a manna shikenan, har me kala da zai canza kalar idon zuwa blue ko gray ds…duk akwai.

Haka nan akwai LASER SURGERY in bakason sanya komi, saide shi yana da tsada, duk ido ɗaya yakan kai dubu ɗari shida zuwa Milyan da ɗaya, shikenan sai a gyara, saide kowa da yadda yake iya ganin results din, galibi anfi yiwa wanda basu kai shekara 35 ba.

Glass de shine mafi sauki da arha, ku dubi hoton ƙasa yadda ta cikin glass komi yake ƙar-ƙar amma ta gefe inda ba tubaran ba dususu bama ka iya gane wasu abubuwan.

Masu ciwon sugar da hawan jini, bayan anyi control dinsu wasu ganin su na dawowa ya gyaru.

______________________________________

ILLAR ƘIN DAUKAR MATAKI GA MASU LARURAR

Idan ka sami kanka da larurar karka bar idanunka haka kaita wahala kana takure su har su riqa zafi da ƙaiƙai, lallai kai kokari kaje kaga likita kuma kabi duk abinda ya baka zaɓi. Ƙin sanya glass da cigaba da zama haka shike haddasa wasu hatsarurrukan a titi saboda direba bai gani sosai.

Hakanan akwana a tashi zaka haɗu da SITIRABISMUS wato jijiyoyin idonka zasu saki saboda halin matsin daka riqa sasu… Don za aga ƙwayar idon mutum ta waskace’ abinda ake kira HARARA GARKE, kaga ga inda mutum ke nuna ma amma inkana kallon kwayar idonsa inda take kallo daban, wanda matsala ce hakan, ai bazaka so a rashin sanya glass ko contact ka zamo haka ba.

Ko kuma illa mafi muni hawan jinin ido wato Glaucoma wacce zata faru akwana atashi saboda matsin da ka riƙa da idon, wannan matsalar ita ke maida mutum makaho na dindindin har abada. Kuma sai an riqa turama allura acikin ido jefi jefi tare da bincikar idon, kullum sai kasa magani, kuma kazo kasa glass ko baka so. Don haka ba wanda muke mas fatan haka, shiyasa gara ai abinda ya dace tun farko.

Ina mai tabbatar muku kafin ma a yanka glass sai anyi gwajin glaucoma dole ne don kar azo ko ta fara samun mutum kila bai zo neman glass da wuri ba… Saida yaga ba dama, ganinsa ya ɓaci da yawa.

Shiyasa wasu wanda a kaiwa glass batare da screening me kyau ba na glaucoma daga baya kan dawo su koka cewa ganinsu ya qara raguwa… Bisa tunanin ko glass ne amma a zahiri glaucoma GARESU.

______________________________________

SHIN GLASS NA ƘARA LALATA IDANU

Magana ta gaskiya karya ne. Ba inda don kana sanya glass za’a ce ganinka qara lalacewa, Infact na gaya muku hawan jinin ido ake tsoratar wa ma wanda suka zauna haka. Kuma babu wasu shekaru da sai ankai za’a sa matukar kwai bukata, wasu tun suna yan shekaru biyu haka suka taso suka ga kansu, kuma har mutuwar su wasu ahaka suke rayuwa da glass, wanka da bacci ne kurum basa yi dashi.

Kunga GLAUCOMA ɗinnan inkai wasa yadda kaga ana ɗauke wutar nepa duhu ya wanzu kai tsaye haka wataran mutum zai iya nemar ganinsa ya rasa, ya makance, kuma ba wata alama kafin faruwar hakan, kana iya kasancewa da ita baka sani ba. Musamman inkasan kwai tarihin matsalolin idanu a family ɗinku ko makanta ai hattara.

Medicated glass muddin kaje ga kwararren likitan idanu (Oftalmolojist) sai yai ma screening ma zai yanka ma dede da ganinka. Illa iyaka tunda de kullum qara girma muke, shima prescription din glass din zaike canzawa tunda ba natural kwayar idon bace, shine zaku ga ahankali ahankali wani yana canza glasses gwargwadon saurin canzawar idon. Kila wannan ake ganin kamar ko ganin ke canzawa.

Kusani ba a glass ɗaya permanent galibi, duk da wasu in akai musu guda shikenan har karshen rayuwa. Wani sai zai karatu ma yake bukata don normal vision garesa, kurum refractive yake fuskanta. Wani na iya shekara 5 zuwa sama da glass ɗaya.

Idan kuma mutum nada halin biyan surgery kamar su PRK bayan angwada anga candidates ne ya cancanci aikin shikenan.
______________________________________

SHIN DUK ME SANYA GLASS WANNAN MATSALAR CE KENAN?

A’a kwai saurin larurori masu jawo a sanya glass amma de kaso 95% cikin ɗari wannan matsalar ce dana tattauna

Fatan bayanin ya ankarar, ya kuma fa’idantar duk da yai tsayi da yawa.

Post a Comment

0 Comments