Ali Nuhu da Adam a zango sunyi Ta’azziyyar mutuwar kamal Aboki

Ali Nuhu da Adam a zango sunyi Ta’azziyyar mutuwar kamal Aboki... 











Innanillahi wa’inna i’laihir raji’un hakika wannan mutuwar ta girgiza al’umma musamman jaruman kannywood da kuma yan uwan sana’ar kamal Aboki domin Mutum ne mai matukar faran faran da kowa bashi da matsala ko kadan dan haka yasa wannan rasuwar rasa ta girgiza kowa mutane sai jimami akeyi akan rasuwarsa

  Acikin wannan halin na rashin dan uwa kamal sai ga wasu manya daga cikin jaruman kannywood musamman Ali Nuhu da kuma Adam a zango sun fito sunyi taazziya wanda hakan ya kara kwantawa da yan uwan kamal Aboki hankali domin idan naku ya rasu kuma kaunar kuga an fito ana yabonsa

Kamal dai ya rasu ne sakamakon hatsarin mota wanda ya ritsa dashi wanda ya janyo sanadiyyar rasa ransa wannan abin ya bawa mutane mamakin kuma ya kada zuciyoyinsu domin kamal Mutum ne mai fara’a., 

                     Kalli video 😭😭👇

Muna addu’a Allah yajikansa da rahama yasa aljanna ce makomarsa Ameen sannan ya bawa yan uwa da iyaye hakurin rasa shi ameen🙏🙏

 



Post a Comment

0 Comments