Yanzu lalacewar hausawa har yakai haka acikin makaran ta ake sheke wannan aya haka…

 Yanzu lalacewar hausawa har yakai haka acikin makaran ta ake sheke wannan aya haka…
















Yanzu lalacewar hausawa har yakai haka acikin makaran ta ake sheke wannan aya haka…

A wani fefen bidiyo dake yawo a shafin sada zumuntar TikTok an gano wani yaro yana taba wata yarinya kamar matarshi,yana rungumar ta,yana abubuwan da basu dace ace ba matar sa ba yake yiwa hakan,koda ace matarsa ce saiya sakaye zaiyi hakan.

 

A kwanakin baya akwai wani hoto daya jawo cece kuce na ganin yadda wata Budurwa ta baje babu kunya samari suna yi mata rubuce rubuce akan kirjin ta.

 

Wannan yana nuna cewa tabbas Iyaye Hausawa dama wandada basu ba,sai an kara gyara damtse domin ceto Yaya daga fadawa irin wannan mummunan halin.

Mutane da dama sunja hankalin hukuma data kama yaron da kuma cin tarar makarantar da hakan ta faru duk dai har yanzu ba’a kai ga tantance a wata jihar abun ya afku ba.

Ba tare da bata lokaci ba zamu saka muku bidiyon domin ku kalla.

 

Allah ya shirya mana baki daya.

Matsalolin Da Ake Fuskanta A Gidan Gala
A ziyarar da wakilinmu ya kai zuwa gidan Dirama, idanunsa ya gane masa abubuwa daban-daban, sannan kunnensa ya jiye masa wasu daga ciki. Akwai abubuwan ban mamaki da ban tausayi gami da ban al’ajabi.

Abubuwan ban mamaki

Daga cikin abubuwan da ya gani na ban mamaki su ne, cin karo da cikakkiyar budurwa wacce da ka kalleta ba sai an yi maka bayani ba ka san gidansu akwai rufin asirin da ba rashi ne ko talauci ya kawo ta gidan ba, sannan kuma kuma za ka ga budurwar da idanka dube ta ka san ba rashin masoyi ne ya kawo ta wannan wuri ba, saboda irin kyan halittar da Allah ya yi mata.

Wata kuma za ka ganta ita ba kyau ba, babu cikakkiyar sutura sannan kuma ga kwarewa a tantiranci, domin a ganinta idan ba ta yi irin wannan zakewar ba kamar ba za ta samu kasuwa ba.

Abin Tausayi

Wani abin tausayi da zai iya sanya hawaye ko kuka shi ne, cin karo da yarinyar da bai kamata a ce an ganta airin wannan wuri ba, wannan ya hada kankantar shekaru, da kuma yunkurin ganin sai kwatanta abin da na gaba dai ta ke yi, mafi muni shi ne, wadanda suke da halayya ta neman mata, ko kuma mazinata su ne ke ta kokarin ganin sun kusance ta.

Za ka ga mutum wanda a haife ya yi jika da ita, amma ba shi da burin da ya wuce ya ga kusance da kwanciya.

“Ka san yaron yanzu ka haife shi ne amma ba ka haifi halinsa ba, ai ina nan zaune take kawo min labarin wasu suna shafe shekara da shekaru ba su dawo gida ba. Ita dai ‘yar uwarta ka ga tana zuwa makaranta ta addini da ta Boko amma dai ita waccan mu nan muna ta addu’a Allah ya shirya mana, na yi kuka a farkon lamarin har na hakura sai dai‘yar uwarta ta ce ba ni hakuri, amma dai ban taba yi mata baki ba,”in ji ta.

To ko yaya ‘yan uwan irin wadannan‘yan mata ke ji a ransu yayin da aka ce ‘yar uwarsu ta shiga irin wannan yanayi? Aminu wa ne ga ita wannan yarinya, ya bayyana wa wakilimmu irin halin da ya tsinci kansa lokacin da ya shigo ya samu mahaifiyarsu na kuka.

“Hankalina ya yi matukar tashi da na shigo gida na samu ummanmu tana kuka, abin da ban saba gani ba, da na tambayi daya kanwar tamu ta fada min abin da yake faruwa, na ji kamar raina zai fita, ana cikin haka sai ga ta ta shigo,babarmu ba ta taba hana ni abu na ki ba amma a ranar da fara dukanta ban ma san tana cewa na bari ba, kuma daga ranar har yanzu ba na yi mata Magana idan ta zo gida,” in ji shi.

Yadda ake gudanar da wasa a gidan a gidan Dirama

Wasannin da ake gudanarwa a gidan ya kasu kashi biyu, wani gidan su kan yi da yamma kuma su yi daddare, wasu kuma sai daya suke yi a rana, wato da daddare kawai.

Ana fara was an bayan Sallar Isha’i, ta yadda za ka ga ‘yan matan gidan sun caba ado sosai, an sanya kida yana tashi gidan kamar ya yi girgiza. Daga nan kuma za ka ga samari na barkowa ta ko ina domin halartar gidan.

Bayan gidan ya yi cikar kwari, sai a samu daya daga cikin masu gabatarwa ya fita da abin magana yanayi wa mahakarta gidan barka da zuwa, sannan zai umarci dukkan ‘yan matan gida da su taho kan babban wani dakali da ake cashe rawa, bayan sun hallara kowa ya gansu, sai kuma ya uamarce su da su je su gaida jama’ar da suka zo domin kallo.

Daga nan ne ‘yan matan za su fantsama cikin jama’a domin gaishe su, a nan ma wata ta kan samu sabon saurayi wanda a lokacin da take cashe rawa zai yi mata liki.

Bayan sun gama da gaisuwar, sai ya sake umartar su da su dawo wannan wuri ta inda za a fara zabar ‘yan matan daya baya daya suna hawa ana sanya musu waka suna kwaikwayon wakar da saurayi kamar dai yadda ake a fim, kuma kowacce dai irin wakar da take so da zarar an sa to duk wanda ya saba zuwa gidan ya san wannan wakar ta wance ce.

Haka su ma mazan suke kowa da tasa wakar, daga nan ne sai samari su fara zuwa suna liki. To wacce ta fi samun kudi za su fara gasa da ta biyunta, a rawa domin a ga wacece ta fi kowacce tara kudi, nan dai za a yi tara kudi.

Amma wacce aka ga ba ta da kowa, sai a fito dai ta kan wannan dabe a ba da sanarwar cewa idan har ba a samu mai fansarta da kudi ba, to za a jika ta da ruwa, kuma za a kawo jakar Fiya wota guda a rirrike, idan aka kirga, 10 babu wanda ya zo yaya yi mata liki, daga nan ne za a fara jika da ruwa har sai jike sharkaf.

To a nan ne idan ta yi dace da masoyi ko kuma wani ya tausaya mata, sai ya zo ya fanshe ta da wani adadin kudi.

Allah Ya Kyauta.

Post a Comment

0 Comments