Waye ya san abin da ‘yaya da ‘yan uwan ku mata suke aikatawa a boye baku sa musu ido ba sai mu?

Waye ya san abin da ‘yaya da ‘yan uwan ku mata suke aikatawa a boye baku sa musu ido ba sai mu? 

 











Waye ya san abin da ‘yaya da ‘yan uwan ku mata suke aikatawa a boye baku sa musu ido ba sai mu? 

Jaruma a fina-finan Kannywood Nafisa Abdullahi, ta bude wuta a shafin ta na Tuwita, inda ta tayi kakkausan martani akan yawan sa ido da kuma kalubalantar mata jarumai da jama’a suke yi.Ganin mutum a talabijin ba shine sanin mutum ba.

A fadar Jarumar tace, kawai mutum dan ya ganka a talabijin, sai kawai ya dauka cewa ya sanka, daga nan sai ya fara shirya yadda ya kamata ace tauraron wasa ya kasance, harma yadda zai yi mu’amala, kai harma yadda zaka yi magana duk mai kallo ne zai tsara maka.

A sakon da ta wallafa, ga abin da tace,

” Kuna da ‘yan uwan mata, wasu ma suna da ‘yaya mata manya, kun san abin da suke abin da suke gudanar wa a rayuwar su a cikin awa 24 a cikin sati? Baku sani ba. Amma baku sa musu ido ba, sai dai kuzo yanar gizo, ku bude wani bakin ku me wari babu mutuntawa, kuna zargi, cin mutuncin wanda baku ma San shi ba. Ana me?

” Kawai sabida mutum baya rayuwar sa yadda ku kuke so ya rayu, to ai kuma ba yadda iyayen ku suke so ku rayu ku ke ba, saboda ina da tabbacin basu san wannan bangaren na rayuwar ku ba. Munafukan banza. Kawai kuyi rayuwar ku, ku bar mutane suyi rayuwar su, ba wani abin takurawa bane kun gane”

Daukaka sai Caccaka


Saboda haka, kamar yadda ake fada ne cewa, zama shahararre yana da farashi, wanda kuma tilas duk wani tauraro ya kwana da sanin haka, cewa mutane dole ne su sami abin fada a kansa, matukar Tauraruwar sa tana haskawa.

Post a Comment

0 Comments