Mutuwar Naziru Sarkin Waƙa A Hatsarin Mota Yanzu Wani Sabon Al’amari Ya Ɓulla....











Biyo Bayan Labarin Dayake Yawo A Kafafen Sada Zumuta Na Cewar Naziru Sarkin Waka Yayi Hatsarin Mota Ya Mutu, Yadda Jarumin Ya Fito Ya Karyata Wannan Lamari.



Duk Da Dai Kuna Sani A Kullum Akan iya Samun Masu Yada Labaran Karya Suna Dangantashi Ga Sanannun Mutane, Kamar Shuwagabanni Ko Kuma Jaruman Kannywood.

Yadda Hakan Ta Faru Akan Jarumi Kuma Mawaki A Masana’antar Kannywood Wato Naziru Ahmad Wanda Ake Kira Da Sarkin Waka.



Jarumin Ya Karyata Wannan Labarine A Shafinsa Na Instgaram Bayan Wallafa Wani Hoto Da Yayi Wanda Aka Hada Hotonsa Da Motar Datayi Hatsari, Sannan Aka Saka Alamar R.I.P Akansa.



.Labarin Ya Janyo Cece Kuce Musamman A Shafin nasa Na Instagram Daya Wallafa Wannan Hoton, Bayan Faruwar Hakan Kuma Sai Gashi Yau Jarumin Ya Sake Wata Wallafa Wanda Yake Jaddada Batunsa Na Cewa Baiyi Wani Hatsari Ba.

Post a Comment

0 Comments