Hira da Matashin daya kashe Mahaifiyar shi a Kano ta hanyar caka mata wuka

 








 Hira da Matashin daya kashe Mahaifiyar shi a Kano ta hanyar caka mata wuka


INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!

Duniya ina zaki damu?

A jiya ne wani labari mara dadi ya karade shafukan sada zumunta musamman ma gidajen rediyo da kuma uwa uba Facebook,cewa an tabbatar da wani Matashi wanda yaje har gidan su inda Mahaifiyar sa take ya daddaba mata wuka a cikin ta da kuma sauran makasar ta.

Labarin yayi matukar tada hankalin mutanan jihar Kano harma da makotan ta.

Sai dai an samu an zanta da Matashin,a inda yake fadin dalilin sa na aikata wannan ta’asar.

Da fari ya fara fadar ba’a gurin ta ya tashi ba kuma sun je jihar Kaduna a inda anan ne Ƴan uwan Mahaifiyar suka dinga yi masa fada akan halin dayake ciki.

Shi kuma ya nuna rashin jin radin hakan,sai dai masu Hikimar zance sun ce daga bakin mai ita yafi dadi,amma kash! Sai dai mu ce rashin dadi a wannan karon.


Ga hirar da mai magana da yawun rundunar Ƴan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa yayi da Matashin.

Ga bidiyon anan kasa,kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!




Post a Comment

0 Comments