Koda Kowa Zai Hana Adam Zango Aure Wallahi Ni Zan Bashi Auren Ƙanwata Mai Shekaru 16, Cewar Matashi Sulaiman

 


Koda Kowa Zai Hana Adam Zango Aure Wallahi Ni Zan Bashi Auren Ƙanwata Mai Shekaru 16, Cewar Matashi Sulaiman.


Sannan kar ku manta sufa mata zuma ne sai da wuta daɗi baya zaunar dasu hakama wuya, nasan in ka taɓa aure to kasan haka in baka taɓa ba to wani naka ya taɓa yi kaje ka tambaye shi zai gaya ma.


Mai karatu kar kace na zaƙe wurin kare Adam, nima haka ya taba faruwa da ni lokacin da nayi Aurena na farko, munyi soyayya sosai da matata ta farko sai da akayi auren komai ya canza nayi haƙurin, amma abin ya ci tura sai da muka rabu lokacin tana goyon ɗan mu mai suna Muh’d Nasir. Na baku wannan labarin ne kada kuce banyi Auren ba amma nazo ina zancen masu aure, to yanzu ma haka inada mata harma ta kusa haihuwa dan haka ina barar addu’a wurin al’ummar Musulmi kan Allah ya sauke ta lafiya.


Adam kayi hakuri komai yayi farko yana da ƙarshe, sannan ka daina ikirarin ka gama aure domin kuwa naka ne ya fito fili don kai Celebirity ne, abu kaɗan idan naku ne kowa zaiji, amma wallahi akwai wanda duk wata sai yayi aure kuma sati biyu ko wata ɗaya zai saki matar kuma ya sake yin wani auren, dan haka bawai ina sonka dayin irin wannan ba ne sai dan ka sani gwara kai har wasu suna haihuwa.


Kuma wannan dalilin naka mai ƙarfi ne, ko nine wallahi matakin da zan ɗauka kenan tunda nayi-nayi anƙi bari.


Kuma hakan shine don ka nunawa duniya kanada kishi don Annabi S.A.W ya ce duk wanda bashi da kishin iyalinsa ba zai shiga Aljannah ba.


Maganata ta ƙarshe shine, wallahi idan duk duniya sun hanaka aure wallahi kazo zan baka ƙanwata ƴar 16 zuwa 17 kazo idan ta yi maka ku sasanta kanku in baka ita, sannan in biku da addu’an Allah ya bada zaman lafiya mai ɗorewa da fatan samun zuri’a ɗayyiba.


Daga masoyinka ma’abocin kallon finafinanka Sulaiman Tanko Babban Nasir (Abul Khairi).

Post a Comment

0 Comments