Adam A Zango Na Neman Addu’ar Masoyansa ‘Yarsa Ɗaya Tilo Tana Kwance Asibiti Rai A Hannun Allah

 



Adam A Zango Na Neman Addu’ar Masoyansa ‘Yarsa Ɗaya Tilo Tana Kwance Asibiti Rai A Hannun Allah.


Jarumin Wanda Ya Samu Karuwar ‘Ya A Shekarar Data Gabata Wanda Mutane Da Dama Sun Tayashi Murna Akan Wannan Samun Haihuwa Ta Wannan Karamar Yarinya, Sai Dai A Yanzu Jarumin Ya Wallafa Wani Bidiyo Daya Dauki Hankalin Mutane.


Yadda Aka Ga Karamar Yarinyar A Kwance Akan Gado An Daura Mata Ruwa Sannan Wata Likita Tana Kusa Da Ita Tana Duba Lafiyar Karamar Yarinyar Kamar Yadda Zaku Kalla A Kasan Rubutun Nan.


Sannam Jarumin Ya Bayyana Cewa Allah Ya Baki Lafiya Baby Na.


A Wani Labarin Kuma Na Daban Ga Jarumin Wanda Ta Faru Akwanakin Baya.


Waiwaye Akan Labarin Ummi Rahab

ABINDA YA RABA TSAKANINSU BA MAI KYAU BANE


Ance mahaifiyar Ummi Rahab itace ta damka amanar ‘yarta wa Adam Zango tun tana yarinya karama bata balaga ba


Kuma Adam Zango ya sakata a fina-finai har duniya ta santa, Ummi Rahab tana hannun Adam Zango har zuwa yanzu da ta balaga ta tumbatsa tana ganin ta kai

Gargadin Naziru Sarkin Waka Ga Masu Zagi


Mahaifiyar Ummi Rahab ta rasu watanni kadan da suka wuce, sai gashi yanzu an wayi gari Adam Zango ya sallami Ummi Rahab, ita kuma tana masa gargadi da ya dena mata batanci imba haka ba zata tona masa asiri


Kamar yadda aka saba Datti Assalafiy ya gudanar da bincike, kuma na samu tabbacin cewa tabbas Adam Zango ya rabu da Rahab, kuma rabuwar banza sukayi, rabuwar uwaka ubanka, na kuma samu bayani akan abinda ya rabasu har ita Rahab tayi barazanan tona masa asiri bayan BBC Hausa sunyi hira da Adam Zango a jiya Alhamis inda ya fadi wata kalma


Na fahimci cewa hakika mahaifiyar Ummi Rahab (Allah Ya jikanta) tayi babban kuskure da ta dauki amanar ‘yarta ta damkashi a hannun wanda shima yana bukatar a bashi tarbiyyah


Gaskiya wannan rayuwa rikon amana tayi karanci, cin amana ya yawaita, ba kowa ake bawa amana ba, wadanda ake ganin suna da tsoron Allah a wannan zamanin suna iya cin amana, balle ‘yan daudu masu lalata tarbiyyan al’ummah.


Malaman tarbiyya Islama sunce, ko halal ce akwai wata halal din da ana barinta don kunya, balle abinda bai halalta ba


Shawaran da zan bamu shine:

Duk wanda Allah Ya bashi mata da ‘ya’ya musamman mata, to yayi kokarin basu tarbiyya ta addini, a wannan zamanin ba’a bada amanar mata, walau matarka na aure ko ‘yarka da ka haifa, idan suka samu tarbiyya da juriya suna sana’a ko mutuwa kayi zasu kubuta da taimakon Allah


Allah Ka tsare al’ummar Musulmin Kasar Hausa daga sharrin ‘yan Hausa film Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum


DAGA Datti Assalafiy

Post a Comment

0 Comments