Rakiya Moussa Poussi ƙwararriya, kuma shaharsrriyar ƴar rawa ce, sannan Jaruma ce a masana'antar Kannywood, kuma haifaffiyar garin Njamena ne dake can ƙasar Nijar, kenan asalin ta ba ƴar Nijeriya ba ce.

 



Tsakanin Rakiya Moussa Poussi Da Soyayya


Daga Shehu Rahinat NaAllah


Rakiya Moussa Poussi ƙwararriya, kuma shaharsrriyar ƴar rawa ce, sannan Jaruma ce a masana'antar Kannywood, kuma haifaffiyar garin Njamena ne dake can ƙasar Nijar, kenan asalin ta ba ƴar Nijeriya ba ce.


Mahaifin ta Shahararren Mawaƙin ƙasar Nijar ne da aka fi sani da suna “Moussa Poussi” kenan za'a iya cewa tayo gado ne.


Rakiya har yanzu tana tsakanin Shekara 20 ne amma bata kai 30 ba, tayi karatun Primary da Secondary ɗin ta duka a can ƙasar Nijar, kafin daga bisani tazo Nigeria inda a farko ta fara ne a matsayin ta na ƴar rawa kasancewar tana da cikakkiyar ƙwarewa akan rawar, don haka Mawaƙi Hamisu Breaker shine mutum na farko da ya fara Featuring ɗin ta a cikin waƙoƙin shi, kafin daga baya wasu suka cigaba da sanya ta a lokacin da ƙwarewar ta da gogewar ta akan rawa suka ƙara bayyana.


Rakiya Moussa ta Shiga harkar finafinai ne inda ta zama Jaruma bayan da tana ƴar rawa hakan na zuwa ne adaidai lokacin da ta koyi Yaren Hausa, saboda ta bayyana cewa koda tazo Nigeria bata jin Hausa ko kaɗan, daga Yaren French sai kuma Zabarmanci kawai take ji.


Saidai abu mafi ɗaukar hankali a cikin tarihin rayuwar ta shine irin halin da ta tsinci kanta a soyayya, wanda mutane da dama basu yarda akan samu irin haka ba, wasu kuma sun yarda ana samu amma ba a wannan zamanin ba, don haka Rakiya kamar yadda ta bayyana a cikin zubar hawaye Masu zafin da ita kaɗai ne zata iya bayyana wannan zafi da raɗaɗin a wata hira da Gabon's TV tayi da ita cewa akwai wanda take so, kuma suna soyayyar su amma kuma daga baya ya rabu da ita, wanda hakan yayi matukar taɓa cigaban rayuwar ta, da kuma zama lafiya da Natsuwar zuciyar ta.


Koda ake mata tambaya akan cewa shin tana bawa wasu samarin damar su kula ta ? Ta amsa da cewa: Eh ta kan bawa samari dama, amma matsalar dake faruwa shine, idan sun zo wurin ta suna tsaka da hira sai ta riƙa ganin surar wancan tsohon saurayin nata kamar gashi nan tsaye yana kallon ta tana hira da wani saurayin, don haka kawai sai tace masa tana zuwa, (Shi Saurayin da yazo wurin ta kenan) to daganan idan ta shiga gida ba zata sake fitowa ba, saidai ya gaji da jira ya tafi, wato tsohon saurayin nata yanai mata Bakan gizo a duk lokacin da take kula wani saurayi.


Koda ake Shawartar ta akan to mai zai hana ta rarrashi zuciyar ta akan soyayyar tashi ta haƙura dashi kawai, sai tace ita ma tayi ƙoƙarin yin hakan, amma ya kasa samuwa, ko ta manta dashi shi ɗin ne dai, don haka ba zata taɓa Mantawa da soyayyar shi ba har ta mutu. “Ba zan taɓa warkewa daga Soyayyar shi ba har In mutu” inji ta


Rakiya Moussa ta bayyana cewa wannan tsohon saurayin nata tana Son Shi, kuma zata iya rayuwa dashi a kowanne hali yake, ko da ba yada hannu ba yada ƙafa, ba yada sana'a, ba yada abinci, ba yada muhalli, kai koda a titi yake kwana ta yarda zata aure shi Indai shi zai aure ta ɗin.


A ƙarshe, ta bayyana fargabar ta da tashin hankalin ta da cewa: “Na san Ni mace ne Indai da rai da lafiya watarana zan yi aure, to babban tashin hankali na shine yadda zanyi rayuwa a gidan wanda zan aura, don ina ganin kamar na cutar dashi ace na aure shi ina gidan shi sannan kuma ina tunanen wani Namiji daban”


To ko me yasa shi wanda take so ɗin ya daina Son ta ?


Bisa dukkan alamu, wanda take so ɗin da farko suna Soyayyar su Tabarakallah Mashallah, a lokacin ba yada Komai, kuma shi ba kowan kowa bane, amma daga baya sai ya samu wata ɗaukaka da daraja don haka sai ya jingine Soyayyar ta a gefe, amma duk da haka, ita tace ta bashi uzuri !

Kamar yadda za'a iya fahimta daga maganar ta shine, yanzu ya taka wani matsayi da ya wuce level ɗin ta don haka shiyasa ya daina soyayya da ita, so wannan shine uzurin da ta bashi.


A lokacin ƙarƙare shirin, Koda ake tambayar ta akan wanne saƙo zata aika masa sai ta kada baki tace: “KAR YA MANTA BAYA” wato wannan shine saƙonta a wurin shi, wanda hakan yake ƙara tabbatar da cewa a baya tayi masa halasci a soyayya, Shikuma lokacin da yakai wani matsayi shine ya juya mata baya.


Bissalam

Post a Comment

0 Comments