Ku Ci Gaba Da Amfani Da Tsaffin Takardun Kuɗi - CBN

 




Ku Ci Gaba Da Amfani Da Tsaffin Takardun Kuɗi - CBN.

Babban Bankin Nijeriya, ya tabbatar wa BBC cewa har yanzu ba a daina amfani da tsofaffin kuɗi ba a faɗin ƙasar.


Wani babban jami'i a CBN ya shaida wa BBC cewa bisa la'akari da umurnin da kotun ƙolin Nijeriya ta bayar na a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin har zuwa ranar 15 ga watan Fabarairu, a domin haka CBN zai bi wannan umurnin har zuwa ranar da za a koma zama a kotun.


Jami'in ya ce a hukumance CBN bai fitar da wata sanarwa ba a kan wannan batun, amma dai bankunan kasuwanci a faɗin Nijeriya ba za su daina karɓar tsofaffin kudi ba har sai bayan wa'adin da kotun kolin kasar ta bayar.


Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Nijeriya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta dakatar da aiwatar da wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na Naira 200 da 500 da kuma 1,000.


Gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar karar, inda suke kalubalantar wa'adin.


Ministan Shari'a kuma babban lauyan gwamnatin Nijeriyar, Abubakar Malami, ne ya ce gwamnatin za ta bi umarnin a wata hira da tashar talabijin na Arise TV mai zaman kansa a Abuja.

Post a Comment

0 Comments