Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’un` Amarya ta Rasu Bayan Gama Daura Mata Aure Yanzu…







Wata amarya ta rigamu gidan gaskiya kwanaki kaɗan bayan tayi aure.Angon amaryar mai suna Idris Elmustapha Daja` shine ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafin sa Facebook. Shafin Linda IkeJi ya rahoto.


El-Mustapha Daja ya auri amaryarsa mai suna Maryam Muhammad Liman, a ranar 6 ga watan Janairun 2023, inda ta amaryar ta rigamu gidan gaskiya a ranar Laraba 18 ga watan Janairun 2023.


An yi jana’izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada a gidan Hajiya Fatima Madugu, dakw akan hanyar Okada, cikin birnin Minna da safiyar ranar Laraba.


Sannan aka kai ta a makwancinta na gaskiya a maƙarbartar Gbakungu cikin birnin na Minna.


Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun. Kwana sha ɗaya da aure, yau na rasa ta. Allah ya jiƙan ki da rahama ya sanya aljannah Firdausi ta zama makoma a gare ki.” Idris ya rubuta a Facebook. 

Post a Comment

0 Comments