Babban Banking Nigeria CBN Ta Bada Damar Karshe Ga Masu Tsohon Takardun Kudi

 



Babban Banking Nigeria CBN Ta Bada Damar Karshe Ga Masu Tsohon Takardun Kudi.


CBN Za Ta Fara Karbar Tsoffin Kudi Tana Turawa Mutane Zuwa Ga Bankinsu Daga Yau Laraba Zuwa Ranar Jumma’a


Bayan umurnin rufe karbar tsoffin kudi da CBN tayi, ta fitar da sabon tsarin da duk wani mai tsoffin kudi zai shigar da kudinshi ba tare da yayi asararsu ba.


Ga tsarin kamar haka;

Da farko mutum zaije CBN na garinsu tare da kash din kudinshi sai yayi generating din Reference Code a Portal din CBN din.


Na biyu ya tabbata yana da Account Number a daya cikin bankunan Najeriya.


Na uku ya tabbata yana da BVN number.


Na Hudu ya tabbata ya tafi da katin dan kasa NIN ko katin zabe Voter’s Card ko daya daga cikin manyan I’D da ake amfani dasu a Najeriya.


Duk abunda mutum bai gane ba Insha’Allah idan yaje CBN zai samu cikakken bayani.


CBN ta sanar da cewa zata karbi tsoffin kudaden ne na tsawon kwanaki uku daga gobe Laraba 15 ga wata zuwa ranar Jumma’a 17 ga wata.


Ina mai bawa al-umma shawara kowa ya daure yaje yakai kudin shi CBN kada mutum yace ai kotu zata tirsasa bankuna su cigaba da karba, abunda ya kamata mu sani shine kotu fa ba ta ajiyan kudi.


In kunne yaji, jiki ya tsira.


A taimaka da share domin sakon ya isa ga al-umma.

Post a Comment

0 Comments