Za A Kai Murja Ibrahim Gwajin Kwakwalwa Don Gano Ko Tana Da Tabin Hankali

 Za A Kai Murja Ibrahim Gwajin Kwakwalwa Don Gano Ko Tana Da Tabin Hankali.




Za A Kai Murja Ibrahim Gwajin Kwakwalwa Don Gano Ko Tana Da Tabin Hankali.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta ba da umarnin yi wa fitacciyar mai amfani da shafin sada zumuntar nan na TikTok a Jihar, Murja Ibrahim, gwajin kwakwalwa domin gano ko tana da tabin hankali.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mamman Dauda, ne ya bayar da umarnin, a cewar Kakakin rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

 

Kakakin ya ce sai an gudanar da gwajin ne za a ci gaba da bincike kan kamun da ’yan sanda suka yi mata.

Idan za a iya tunawa, Aminiya ta rawaito muku yadda ’yan sanda suka kama Murja ranar Lahadi, bayan sun karbi korafi a kan yadda take amfani da shafin wajen zage-zage da kuma bata tarbiyya.

 

An kama ta ne a otal din Tahir Guest Palace da ke Kano, tana tsaka da shirye-shiryen gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarta.

Majalisar Malamai ta Jihar Kano ce dai ta kai korafi kan Murja bisa yadda ta ce bidiyoyin da take wallafawa a shafin nata sun saba wa koyarwar addinin Musulunci.

 

Sai dai daga bisani ta yi alkawarin cewa daga yanzu ta daina zage-zagen kamar yadda aka bukata.

Kamun nata dai ya janyo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda wasu ke kiran da a gaggauta sarkinta, wasu kuma na cewa ya zama wajibi a hukunta ta don ya zama izina ga wasu.

Post a Comment

0 Comments