Bidiyo: Mansura Isah ta bayyanawa duniya dalilin dayasa ta kama masu batawa yarinyar ta suna suna damfarar mutane

 Bidiyo: Mansura Isah ta bayyanawa duniya dalilin dayasa ta kama masu batawa yarinyar ta suna suna damfarar mutane.





Tsohuwar fitacciyar jaruma a masana’antar kannywood Mansura Isah tsohuwar mata ga mawaki kuma Dan Siyasa Sani Danja ta bayyanawa duniya wasu dalilai da yasa tasa aka kamo mata masu amfani da sunan yarinyar Iman Sani Danja  suna ci mata zarafi.

Mansura din tayi korafi tun a kwanakin baya akan masu yin hakan da suyiwa Allah suyiwa Annabi su dakatar su dena,amma basu ji ba sukaci gaba,hakanne yasa ta dauki matakin kamo su har inda suke.

Yanzu haka tace an tura yaran gidan maza domin jiran Shari’a din.

Ga duk masu bibiyar shafukan sada zumunta sun san daman ana yawan samun sojojin gona masu amfani da sunan wani domin su bata masa suna ko kuma su saka hajarsu.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakkiyar hirar da mukayi da jarumar anan kasa.


Post a Comment

0 Comments