Yadda zakuyi hadin maganin karacin sha’awa domin biyawa iyali bukata a kan gado

Yadda zakuyi hadin maganin karacin sha’awa domin biyawa iyali bukata a kan gado...












Yadda zakuyi hadin maganin karacin sha’awa domin biyawa iyali bukata a kan gado.

Sha’awa tana zama masifa a wurin Dan Adam musamman idan tana haddasa aikata alfasha ko kuma wadansu munanan ayyukan da suke abinkyama cikin addini, da kuma al’umma baki daya.

Sha’awa, haka zalika kuma tana daya daga cikin alamun lafilyayyen mutum mace ko namiji ta hanyoyi da dama, tun daga kan wasa kafin jima’i har zuwa lokacin da ake jima’i domin samun ishesshiyar gamsuwa.

Bisa wannan dalili ne yasa zamu kawo muku hanyar da zaku bi domin magance wannan matsalar ta fuskoki da dama.

Ga abubuwan da zaku nema domin hadin maganin.

(1) Garin Habbatus Sauda

(2) Garin Yansun

(3) Man YansunBayan kun nemo wadannan abubuwan ga yadda zakuyi hadin nasu.

Zaku samu garin Habba da garin Yansun ku hadesu guri daya sai ku tafasa idan ya tafasa sai ku tace ruwan ku zuba man Yansun din a cikin ruwan, sannan ku juya sai kuna sha.

Ku yawaita sha kuma zaku sha wannan hadin har na tsawon sati biyu, to insha Allahu zaku samu biyan bukata.

Kamar yadda kuka sani ita dai sha’awa ba karamin taka rawar gani take ba ga ma’aurata daga Mace har Namiji, domin wasu dalilin rashin ta zamantakewar auren nasu baya karko.

Da dama wasu ma’auratar suna kokawa kan rashin sha’awa musamman a yayin da zasu raya sunnah, sai kaga maigida ko matarsa wani daga cikin su sha’awar tasa taki motsawa daga nan kuma sai bacin rai ya shiga tsakani.insha Allahu in dai kuke yawaita yin wannan hadin maganin da muka kawo muku zaku sami biyan bukata a bangaren sha’awa, domin kuwa ba lallai ne tana dauke muku ba ako wane lokaci.

Allah ya bamu sa’a.

Post a Comment

0 Comments