Wadannan Abubuwan Suna Tasiri Wajen Lalacewar Auren Hausawa A Yanzu Cewar Fauziyya D Suleiman

 Wadannan Abubuwan Suna Tasiri Wajen Lalacewar Auren Hausawa A Yanzu Cewar Fauziyya D Suleiman..




Fauziyya D Suleiman Wacce Daya Ce Daga Cikin Manyan Mata A Kungiyar Creative Helping Needy Foundation (CHNF) Wato Kungiyar Kula Da Marasa Karfi Da Kuma Marayu, Ta Bayar Da Shawara Ga Iyayen Amarya Bayan Anyi Aure.

Fauziyya D Suleiman Ta Wallafa Wata Doguwar Bidiyo A Shafinta Na Instagram Yadda Take Shawartar Iyayen Amarya Su Kula Da Korafin Da Ake Kawo Musu Domin Samun Zaman Lafiya Acikin Gida.

Duk Dai Acikin Bayaninta Tace Sau Dayawa Ana Kawo Musu Korafi Ko Kuma Amarya Ta Kawo Korafin Mijinta, Yana Yi Mata Wasu Abubuwa Marasa Dadi Ko Baya Kyautata Mata, Maimakon A Tsaya A Zaunar Dashi Da Ita Ayi Musu Fada Sai A Kyaleta Sannan Ace Mata Zaman Aure Sai Hakuri.

Sannan Ta Kara Dacewa Akwai Matsalolin Da Dole Sai Ana Bibitar Al’amarin Ana Gyarawa Domin Samun Zaman Lafiya A Bangaren Aure, Saboda Wannan Nuna Halin Ko In kula Da iyaye Sukeyi Ga Amarya Bayan Aure, Yana Tasiri Wajen Rushe Auren Baki Daya.

Haka Zalika Kamar Yadda Miji Zai Kawo Karar Matarsa Tana Yi Masa Abunda Bai Dace Ba, A Zaunar Da Ita Ayi Mata Nasiha Toh Hakama Ita Amarya Idan Takawo Karar Miji Yana Da Kyau A Zaunar Dashi Ayi Masa Nasiha, Domin Rashin Yin Hakan Kamar Tauye Hakkine Ga Matar.

Domin Kuwa Yawanchi Matsalolin Da Ake Fuskanta A Bangaren Aure Yanzu, Yana Daga Rashin Fahimta Da Kuma Wannan Abunda Fauziyya D Suleiman Tayi Tsokaci Akansa.

Saboda Akwai Maza Dayawa Wadanda Basu Da Kirki, Idan Mace Ta Kawo Kararsu Sai Aki Goyon Bayanta Anace Mata Zaman Aure Sai Hakuri, Daga Karshe Sai Abun Yakai Matar Ta Nemi Saki Da Kanta Shikuma Mijin A Take Ya Sake Ta, Amma Idan Ana Sauraron Korafin Da Suke Kawowa Anayi Musu Sulhu Gaba Daya Toh Za’a Samu Cikakken Zaman Lafiya.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Al’amari Dayake Faruwa Na Rabuwar Aure A Arewachin Nigeria, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Post a Comment

0 Comments