Tafaru ta kare kisan Abdul jabbar shiga kaga abun da Daliban sa suke yi shiga nan

Tafaru ta kare kisan Abdul jabbar shiga kaga abun da Daliban sa suke yi shiga nan..














Wata sabuwa ku kuran ta abun da Daliban Abdul jabbar suke cewa akan yake masa hukuncin kisa da aka yi saka makon batancin da yake yi ga fiyayyan halitta Annabi Muhammadu S.A.W ku kuran ta labarin anan kasa kadan.

Almajiran Sheikh Abduljabbar sun ce akwai abubuwan da basu gamsu da su a cikin hukuncin kotun da yanke, wannan na zuwa ne bayan hukuncin da mai shari’a na babbar kotun musulunci ya same da laifin aibata fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Kamar yadda wa’azinsa da shari’ar ke cike da cece-kuce haka ma hukuncin kisan da aka yanke masa ta hanyar rataya, shi ma a yanzu yana tattare da wannan kace-na-ce din.

Yayin da kusan mutane da dama suke ganin hukuncin ya dace da tuhume-tuhumen aikata sabo akan fiyayyen halitta da aka samu Sheikh Abduljjabar da laifi, wasu kuma musamman wasu dalibansa suna cewa ba’a yi la’akari da hujjojin da malamin nasu ya gabatar a gaban kotun ba a wajen yanke hukuncin.

Sai dai kuma daliban nasa sun shaidawa BBC cewa su masu biyayya ne. Amma a cewarsa shari’a tana cike da ayoyin tambaya, wannan hukunci na yau dai, shi ne kusan babban labarin da ya karaÉ—e ba kawai jihar Kano ba, har ma da sassan musamman arewacin Najeriya.

Akasari dai hukunci irin wannan ya kan zamo babban kalubale musamman ga mahukunta wajen zartar da shi, babbar kotun musulunci dai ta ce yana da kwana talatin ya daukaka kara.

Yanzu dama ta rage ga Sheikh Abduljabbar, duk da ya ke har lokacin da ake yanke masa hukunci yana cewa bai aikata laifi ba, sai dai batun mika wuya ga hukuncin yanzu za a zuba ido a gani ko zai yi amfani da wannan damar ko akasin haka, labari tsarawa daga

Post a Comment

0 Comments