Mutuwar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din LABARINA Yanzu Akayi Cikakken Bayani Akan Mutuwar Tasa

Mutuwar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din LABARINA Yanzu Akayi Cikakken Bayani Akan Mutuwar Tasa..







Mutuwar Nuhu Abdullahi Wato Mahmud Acikin Shirin Film Din LABARINA Yanzu Akayi Cikakken Bayani Akan Mutuwar Tasa.

A Wata Doguwar Hira Da Akayi Da Aminu Saira Wato Babban Darakta Na Cikin Shirin Film Din Labarina mai Dogon Zango Ya Bayyana Dalilin Dayasa Jarumin Da Akafi so Ya Mutu Acikin Shirin.

Kamar Yadda Gidan Jarida Voa Hausa Tayi Da Aminu Saira Ta Wayar Salula Ya Bayyana Dalilai Masu Kwari Akan Mutuwar Mahmud, Fitaccen Jarumi Dayake Taka Muhimmiyar Rawa Acikin Film Din.

Ga Masu Bibiyar Shirin Film Din Labarina Mai Dogon Zango Zasu Ga A Wannan Satin Wato A Zango Na Uku Ansamu Wani Rudani Wanda Mutane Da Dama Suna Tambaya Akan Abun Da Kuma Menene Dalilin Faruwar Hakan.

Abunda Ya Faru Ba Komai Bane Face Yadda Akaga Jarumi Mai taka Muhimmiyar Rawa Acikin Film Din Wato Mahmud Wanda Mafi Akasarin Mutane Suna Kallon Film Dinne Dominshi Duba Da Yadda Yake Gudanar Da Aiki Acikin Film Din Yana Burge Masu Kallo.

To Kwastam Sai Aka ga Ya Mutu Acikin Film Din, Nan Take Mutane Sukayi Ta Tura Tambayoyinsu Zuwa Ga Shafukan Sada Zumunta Domin Sanin Dalilin Mutuwartasa da Kuma Rashin Jin Dadinsu Ga Faruwar Hakan.

Mamallakin Shirin Film Din Wato Malam Aminu Saira Ya Bayyana Dalilin Mutuwar Tasa Da Kuma Yadda Shirin Zai Sa Gaba, Baya Da Haka Yayi Tsokaci Akan Abunda Mutane Suke Tambayarsu.

Acikin Bayaninsa Ya Bayyana Cewa Mutane Suyi Hakuri Suga Karshen Film Din Tukunna, Domin Shi Film Me Dogon Zango Ba’a Yi Masa Hanzari Sai Dai A Tsaya Na Bibiyarsa Har Akai Lokin Da Aka Gamashi, Daga Lokacin Da Akace Film Yazo Karshe To Daga nan Mutum Zai Tabbatar Da Abunda Yake Zargi Ko Kuma Yake so Ya Sani.

Yan Jarida Sunso jin tabakinsa Akan Cewa Shin Mahmud Mutuwa Yayine Da Gaske Ko Kuma Zai Dawo Nan Gaba? Amma Basu Samu Cikakkiyar Amsa Daga Bakin Daraktan Ba Wato Aminu Saira, sannan Ya Bayyana Cewa Mutane Su Kara Hakuri Zasu Ga Abunda Zai Faru A Sauran Zangon Dazai Zo Nan Gaba.

Ga Bidiyon Sai Ku Kalla.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Bidiyo, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Ku Karanta Wannan Labarin:

Karin bayaniAfricanwin.com.ng  

Post a Comment

0 Comments