Maganin karfin mazakuta kankancewar azzakari da saurin kawowa da karin ruwan maniyyi

Maganin karfin mazakuta kankancewar azzakari da saurin kawowa da karin ruwan maniyyi..







ABUBUWAN DA ANGO ZAI FARA AMFANI DASU KAFIN AUREN SA.

ka samu habbatussauda, kustul Hindi, hulba, haltil, jinsen ka hadasu da dan yawa Ka niqasu sai ka dinga shansa kullum a shayi kamar teaspoon sau 3 a rana ko.


Kuma kadinga dafa cokali 2 a shayi kamar filas 1 kadinga sha Kuma abin mahadin kada kasa suga sai dai mazar kwaila ko Zuma marar hadi.


Zaka Fara amfani da maganin sanyi mai kyau da maganin basur kana sha lokaci lokaci.

CIKAMAR DA TAKE SA QARFIN JIMA’I.

Akwai wasu abinci da idan akayi anfani dasu suna sa kuzari ga da namiji misali Kamar su:

citta, barkono ayaba, salak, dabino, alaiyahu, albasa, wannan kamai sune abubuwan da zakana ci idan kana shirin aure da bayan aurenka.

CIMAKAR DA TAKE QARA QARFIN MARAINA.

Gyada, Garin gero, yayan itaciya, man zaitun, gayyanyaki, wake, Karas , dankalin hausa, ‘yayan gurji da ‘yayan kabewa da kwai na kazar gida.

CIMAKAR DA TAKE QARA RUWAN MANIYYI.

Ayaba ,tumatur, ‘yayan kabewa, gyada da gyadar yarabawa, tafarnuwa, kana anfani da wadanan kafin aure da Kuma bayan auren ka.

CIMAKAR DA TAKE DA JIN DADIN JIMA’I.

Citta mai kwaya, ayaba, gyada, zuma, lemon zaki, kubewa dabino busasshe, aya, yayan kabewa.

ABUBUWAN DA ANGO ZAI BARI KOMA YADAINA SHA.

Suger, lemon kwalba dana roba, shan taba, shangiya, duk wani nau’in lemo da aka sawa suga ko kafi suga, dan zaki, sweetener, duk sai ka barsu idan kanason ka zama cikakken namji.

ABUBUWAN DA SUKE SA RAUNIN AZKARI.

Ciwon zuciya, hawan jini, yawan kitse a jiki, kunburin maraina, rashin samun bacci, kankancewar maraina, ciwon suger, shan suger, tunani.

Wannan matsaloli dana lissafa toh idan kasan kana dasu ka fara neman magani kafin aurenka.

Allah ya bamu sa’a

Post a Comment

0 Comments