Ko dai bata son shi ne? Mutane sunyi ca akan hotunan nan na kafin Aure

Ko dai bata son shi ne? Mutane sunyi ca akan hotunan nan na kafin Aure..












Wasu zafafan hotuna Kenan da suka karade shafin sada zumunta na Facebook kenan,na wani Ango da ba’a bayyana sunan sa ba.


An gano Angon a cikin hotunan yana sumbatar Amaryar tasa,sai dai kuma inda gizo yake sakar itace,an gano Amarya ta turbune,hakan tasa mutane sukayi ca bayan ganin hotunan sun burge su.

Wasu fadi suke,”anya kuwa tana sonshi kuwa?”

Wasu kuma yanke baki sukayi suna fadin,”Daga ganin wannan ba Auren Soyayya bane ba.”

Yayin da wasu fadi suke cewa”,Amaryar kunya take ji,shi kuwa gogan abunsa kawai yake yi”


Haka dai mutane da dama masu mabanbantan ra’ayoyi sukaci gaba da bayyana ra’ayoyin su a shafin na Facebook.

Ga Hotunan kamar haka,Allah ya basu zaman lafiya

Post a Comment

0 Comments