Ina Kokarin Ganin Na Zama Ta Gari, Ya Allah Ka Yafe Min Kura-kuraina, Ka Dawo Da Ni Kan Hanya Madaidaiciya, Cewar Safara’u

 Ina Kokarin Ganin Na Zama Ta Gari, Ya Allah Ka Yafe Min Kura-kuraina, Ka Dawo Da Ni Kan Hanya Madaidaiciya, Cewar Safara’u.



Ina Kokarin Ganin Na Zama Ta Gari, Ya Allah Ka Yafe Min Kura-kuraina, Ka Dawo Da Ni Kan Hanya Madaidaiciya, Cewar Safara’u

Kamar dai yadda jaridar Rariya ta rawaito, mutane da dama sun bayyana ra’ayoyin su akan batun Safara’u din kamar haka:

Absan Abu Ahmad yace “Muma hakane fatanmu, duk wani kunfar baki da rubuce-rubuce da mukeyi Allah yagani ba munayin hakan bane don ɓatamiki suna/ko tozartaki, a’a munayin hakanne don koda wasu sunada burin shiga irin harkar da kikeyi su fasa, sbd ba harka bace wadda mutum zaiso ace kanwarshi ko ƴarshi sun faɗa, Allah ya taimakemu baki daya, yaɗoramu akan hanya madaidaiciya 🙏”

Muhammad Ibrahim yace “Masha Allah Tabarakallah. Indai wannan maganar da gaskene Wallahi ina cikin wadda zasuyi farin ciki matuka saboda har Ga Allah halayennata suna damu sosai. Ina rokon Allah Ya shirya da ita Ya shiryar da dukkan sauran masu halaye irinnata Ya shiryar damu gabadaya Allahumma amin.”

Farida “Yar Mama tace “Duk Wanda ka gani shiryayye toh ba dabarar sa bace ko wayonsa yasa Allah ya shiryar dashi, kawai yardar ubangiji ne,kema muna tayaki da addu’a Allah ubangiji ya shiryaki da mu baki daya yasa mu cika da Imani ya kuma baki miji nagari tare da mu,suma mazan ya basu Mata na gari 🤲”

Post a Comment

0 Comments