Idan kana so ka gane macen da tafi ni’ima wanda zakanajin ta kamar zuma idan kun yi aure kalli video Bayan bayani kan mas’alolin da suka gabata kan batun karfafa alaka tsakanin ma’aurata sai kuma bukatar fadadawa (MUHIMMAN MAS’ALOLI) sakamakon cewa wannan bangaren shi ne madarar zaman rayuwar ma’aurata don haka na kara da wadannan bayanai masu muhimmanci wurin karfafa alakar rayuwar aurataiya. 1-Shelanta Soyaiya

 Idan kana so ka gane macen da tafi ni’ima wanda zakanajin ta kamar zuma idan kun yi aure kalli video..







Bayan bayani kan mas’alolin da suka gabata kan batun karfafa alaka tsakanin ma’aurata sai kuma bukatar fadadawa (MUHIMMAN MAS’ALOLI) sakamakon cewa wannan bangaren shi ne madarar zaman rayuwar ma’aurata don haka na kara da wadannan bayanai masu muhimmanci wurin karfafa alakar rayuwar aurataiya.

1-Shelanta Soyaiya

Bayan soyaiya da kaunar da ma’aurata suke nuna wa juna, sai kuma baiyanar da wannan soyaiyar a fili cikin kalmomi masu dadin ji a kunne. Musulunci ya karfafi gaya wa mace ina son ki, masoyiyata, ina kaunar ki, da sauran kalmomin da suke nuna kauna da soyaiya tsakanin ma’aurata. Ruwaya tana gaya mana cewa idan mutum ya ce wa matarsa “ina son ki” to kalma ce da ba zata iya mantawa da ita ba har abada[1]. Don haka ko da kuwa akwai soyaiya to da bukatar a furta ta a lafazi mai dadi.


 


2-Girmama Juna


Girmama Juna yana daga cikin abin da zai karfafa alakar rayuwar tare tsakanin ma’aurata, namiji yana karfafa mace, haka ma mace tana karfafa namiji ne ta hanyar girmama juna. Wannan yana da matukar muhimmanci musamman idan akwai yara da suke son tarbiiyatarwa ta yadda ‘ya’yansu zasu tafi gidan aurensu suna dauke da wannan koyarwa mai muhimmanci.

Post a Comment

0 Comments