Innalillahi Murja Ibrahim Kunya Tayi Bello Turji Zagin Kare Dangi
Wasu Alamomi Da Zaka Fahimci Mace Na Sonka:
$ads={1}
Ba ko wace mace bace take iya buga kirji ta tinkari namiji tace masa tana sonsa ba. Sai dai idan na miji nada natsuwa cikin sauki zai fahimci wasu halayen da macen datake sonshi zata rika nuna masa domin bashi damar shi ya furta mata kalmar so.
$ads={2}
Ga wasu alamun da zaka iya fahimtar mace na sonka amma tana kaiwa kasuwa.
1: Mace idan tana sonka duk lokacin da kuka hadu sai ta tambayeka yan matanka.
Idan kace mata babu ta jaka da wata hiran idan kuma kace akwai zata sauya fuska tace maka ka gaisheta tayi tafiyanta.
Wannan ba zai hanata sake tambayarka idan kun sake haduwa ba. Don haka kana ganin mace tana yawan tambayarka budurwarka ko Yan matanka, alama mu ne tana sonka.
2: Mace Idan tana sonka amma tana kunyar furta maka zaka ga tana yawan zuwa maka da matsalolin da kodai tana neman shawaranka ko kuma tana so ka warware mata su da kanka.
Bini bini zata bukace ka tace tana da magana da kai. Da zaran ka fahimci haka idan kana sonta kawai ka furta daman abunda take nema kenan.
3: Mace idan tana sonka tana kunya fadamaka zata yi duk yadda zata yi har sai ta gayyaceka inda take. Mace idan bata son namiji bata burin ganinsa a inda take.
Don haka kana ganin mace ta nace da tana son sai ka zo inda take abokina ka samu shiga ne.
4: Idan mace tana sonka zata rika kunyarka. Duk rashin kunyarta idan kana waje akwai abubuwan da bazata iya yinsu ba.
Nuna maka kunya matuka alamu ne da yake nuna cewa macen tana sonka.5: Idan mace na sonka babu zato babu tsammani zaka ga ta kawo maka wata kyauta ta musamman. Wannan kyuatar kuma koda wani abune da ita ke sarrafashi ko kuma saye zata yi.
Idan mace na sonka idan ta tashi yi maka kyauta kawai sai da ka gani amma ba tambayarka zata yi ba.6: Mace idan tana son namiji duk yadda aka bata mata rai tana ganinsa zata saki fuska. Idan mace na sonka tana kasancewa ne cikin farin ciki a duk lokacinda take tare da kai.
Mace mai sonka amma tana jin nauyin furta maka, zata rika burin ganin kullum Kuna haduwa kuma kuna samun lokaci mai tsawo kuna zantawa.
Kana ganin hakan to fa sonka ake yi.
7: Duk rashin yin maganar mace idan tana son namiji za kaga itace take soma yi maka magana. Kuma a hirar taku maganganunta sai sun naka yawa.
Mace duk miskilancinta tana haduwa da nanijin data so zata saki ji da fuska tana zuba labari da wanda yasanta da miskilancinta zai zo ya ganta zai sha mamakin ganin yadda ta saki jiki a gaban wanda take so .
8: Idan mace tana yawan yi maka shagwaba, da yarinta idan kuna tare, wannan macen sonka take. Kuma alamune take nuna maka na zaka iya sarrafata yadda kake so a matsayin mai sonka.
Don haka kana ganin hakan idan kaima kanada muradi sai ka shirya tura manya.9: A duk lokacinda ka fahimci idan kana tsaye da wasu mata bata gaisheka, to ka tabbatar da sonka take yi.
Ita macen da bata ra’ayin namiji bata damuwa da su wa yake tsaye dasu maza ne ko matane. Babu ruwanta da abunda kuke cewa. Kuma hakan ba zai hanata tsayawa ku gaisa ba.
Amma ita macen datake sonka tana ganinka da mace ko kaine ka gaisheta da wuya ta amsa maka gaisuwan. Kuma bazata taba tsayuwa kuyi hira kamar yadda kuka saba yi idan bata ganka da kowa ba.
Da zaran ka fahimci hakan a wajen mace to sonka take amma bazata iya furta maka bane.10: Mace idan tana sonka amma ta kasa fadamaka zaka ga a kullum taci kwalliya bazata cire wadannan kayan ba sai tayi duk yadda zaku hadu ka ganta ka yaba.
Mace mai sonka bata so taci adonta ya sha iska a banza wanda take so bai gani ba.
#itsangayaramalamtonga
#sirrinrikemiji
Da fatan maza zasu fahimci cewa akwai mata da dama da suke sonsu amma sun kasa fadanusu su kuma sun kasa fahimtar hakan.
Da fatan yanzu zasu gano irin wannan inkiyar daga matan dake sonsu suna boyewa.
0 Comments